Abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da Buhari yayinda ya cika shekaru 78 yau

Abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da Buhari yayinda ya cika shekaru 78 yau

A yau 17 ga watan Disamba, 2020, Shugaban kasan Najeriya na demokradiyya na hudu, Muhammadu Buhari, ya cika shekaru 78 a duniya.

Domin taya shi murnar wannan rana, Legit Hausa ta tattaro muhimman abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da shugaban kasan:

1.An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga Disamba, 1942 a Daura, Katsina ga iyalin Hardo Adamu, mahaifinsa, da Zulaihat, mahaifiyarsa.

2. Shine 'da na 23 cikin 'yayan mahaifinsa. Mahaifiyarsa ta raineshi lokacin da mahaifinsa ya rasu yana mai shekaru hudu.

3. Shugaba Buhari ya yi karatu a Katsina. Sannan ya shiga horon Soja a Kaduna, Birtaniya, Indiya da Amurka.

4. Shugaba Buhari na cikin wadanda sukayi juyin mulkin Yakubu Gowon a 1975 kuma aka nadashi gwamnan yankin Arewa maso gabas (yanzu Borno) a shekaran.

5. Janar Olusegun Obasanjo ya nada shi kwamishanan arzikin man fetur lokacin da ya zama shugaban kasan mulkin Soja bayan mutuwan Murtala Mohammed a 1976.

6. A 1977, Buhari ya zama Sakataren gidan Soja a hedkwatan gwamnati

7. Tsakanin 1982 da 1985, shugaba Buhari ya zama shugaban kasan na mulkin Soja

8. A 2003. Buhari ya yi takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APP amma ya sha kashi hannun Olusegun Obasanjo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU DUBA: Gwamnan Legas ya bada umurnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandaren jihar

Abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da Buhari yayinda ya cika shekaru 78 yau
Abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da Buhari yayinda ya cika shekaru 78 yau Credit: @APCNigeria
Source: Twitter

KU KARANTA: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona

9. A 2007, Buhari ya sake takara kuma ya sha kaye hannnun marigayi Umaru Musa Yar'adua

10. Hakazalika a shekarar 2011, ya sake takara karkashin jam'iyyar CPC kuma ya sha kasa wajen tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

11. Bai gajiya ba, Buhari ya sake takara amma yanzu karkashin jam'iyyar APC a 2015 kuma ya lashe zaben bayan kayar da Goodluck Jonathan.

12. Nasarar Buhari ya zama tarihi saboda shine mutumin farko da ya taba lallasa shugaba mai ci a tarihin siyasar Najeriya

13. A 2019, shugaba Buhari ya sake lashe zabe inda ya lallasa Atiku Abubakar na PDP

14. Shugaba Buhari yana auren Aisha Halilu (Aisha Buhari) tun 1989, kuma Allah ya azurtasu da yara 5.

15. Amma Buhari na da wasu yara 5 da tsohuwar matarsa, marigayiya Safinatu Yusuf.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel