An kashe soja daya, an raunata guda yayin kokarin ceton dan kasar waje da 'yan bindiga suka sace

An kashe soja daya, an raunata guda yayin kokarin ceton dan kasar waje da 'yan bindiga suka sace

- An tsinci gawar wani soja da wani farar hula a wani daji da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo

- Kazalika, wani babban soja da wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC sun samu raunuka

- Hakan ta faru ne a kokarin ceto wani dan kasar India da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da shi a Ibadan

Rundunar yan sanda a jihar Oyo ta sanar da cewa ta gano gawar wani soja ɗaya da ta farar hula a wani daji dake Ibadan.

A cewar rundunar, an kashesu ne yayin da suke neman wani ɗan ƙasar waje da masu garkuwa suka sace, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ne ya bayyana hakan ranar Litinin.

KARANTA: Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT da suka maye gurbin SARS

Ya kara da cewa wani babban soja mai mukamin Laftanal da jam'in tsaro na "Civil Defence Corps" na daga cikin waɗanda suka ji rauni a musayar wuta da jami'an tsaro suka yi da masu garkuwa.

An kashe soja daya, an raunata guda yayin kokarin ceton dan kasar waje da 'yan bindiga suka sace
An kashe soja daya, an raunata guda yayin kokarin ceton dan kasar waje da 'yan bindiga suka sace
Source: UGC

A cewarsa, masu garkuwa da mutane sun sace Hassan Mills, mai gidan gonar Panorama Farm a Mekun dake yankin Oke Alaron a garin Ibadan, a kan hanyarsa ta zuwa gidan gona.

Ya kara da cewa, baturen yan sandan yankin Oke Alaro tare da tawagar jama'arsa, sun kutsa cikin dajin da maharan suka tsere don kwato mutumin da suka sace.

KARANTA: Da ma can bai cancanta ba; a karshe, Ganduje ya bayyana dalilin nadi da tsige Sanusi

Daga baya wata tawagar rundunar jami'an tsaro ta musamman ta tunkari wajen da 'yan ta'addar suka kutsa a cikin dajin.

A nan ne wani soja ya samu rauni a kafarsa ta dama sakamakon musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da barayin mutanen.

Sai dai, Kakakin ya nuna takaicinsa bisa yadda yan ƙasashen waje ke zirga-zirga a yankin ba tare da neman shawara daga jami'an tsaro ba.

Legit.ng ta rawaito cewa wani kwararre a fannin tsaro, Dr Ona Ekhomu, ya bukaci gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da ya shige gaba, ya zama jagora, wajen ceto ɗaliban da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta yi ikirarin sacewa.

Ya ce, Masari ke da babbar rawar takawa wajen ceto yaran da aka sace, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

A cewar Dakta Ekhomu, "duk rana ɗaya da ta wuce, tamkar kara nesa da damar ceto wadancan yaran ne."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel