Yadda za ka tabbatar da matsayin rijistan layinka domin gudun kada NCC ta toshe ka

Yadda za ka tabbatar da matsayin rijistan layinka domin gudun kada NCC ta toshe ka

A ranar Alhamis, 12 ga wata Satumba, Dr Isa Pantami, ministan sadarwa yace an umurci hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da ta toshe layukan waya marasa rijista wanda sun fi sama da miliyan tara.

Hukumar ta NCC, a cewar ministan, ya zama dole ta tabbatar da cewar an toshe layukan mutanen da basu yi rijista ba har sai sun bi ka’ida ta hanyar bin tsarin da ya kamata wajen yin rijista.

Domin bin wannan umurni, yan Najeriya wadanda layukan wayansu bai da rijista na gab da rasa dammar amfani da lambobinsu, ta hanyar haramta masu kira.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Hatsarin mota ya hallaka mutane 13 tare da jikkata wasu 11 a Nasarawa

Idan kana son tabbatar da ko lambar wayarka na da rijista yadda ya kamata, ka lambobin da za ka danna:

MTN - danna *789*1#

Airtel - danna *746#

9mobile - danna 746 ko 200

Glo - aika REG zuwa ga 746 ko 3456

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Pantami ya ce a halin da ake ciki yanzu akwai kimanin layukan wayar salula miliyan 9 da ake amfani da su a Najeriya ba tare da rajista ba.

Isa Ali Pantami ya ba wa hukumar kula da ma’aikatun sadarwa ta kasa wato NCC umarnin cewa su gaggauta rufe layukan har sai masu layin sun bayyana kawunansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel