Na fuskanci kalubale a 2015 saboda alheran da nake son kawowa Najeriya, Jonathan

Na fuskanci kalubale a 2015 saboda alheran da nake son kawowa Najeriya, Jonathan

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan yace yasha caccaka a 2015

- Yace abokansa da masu bambancin ra'ayi a siyasa dashi sun tozarta shi kuma cutar dashi

- A cewarsa, duk abinda yayi a lokacin, gani sukeyi bai iya ba, amma ya yafe wa kowa

Bayan Dino Melaye ya baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri, akan yadda ya tsaya kai-da-fata wurin ganin sun saukeshi daga mulki, Bala Mohammed ya sara wa Jonathan, har yana kiransa da sadauki.

A ranar Talata, Jonathan yace wasu abokansa da abokan hamayyarsa na siyasa sunyi masa mummunan zato kafin zaben shugaban kasa na 2015 saboda dagewarsa da burinsa na ciyar da kasarnan gaba.

Duk da hakan, yace bai rike kowa a zuciyarsa ba, duk da kushe da zagon kasar da akayita masa.

Na fuskanci kalubale a 2015 saboda alheran da nake son kawowa Najeriya, Jonathan
Na fuskanci kalubale a 2015 saboda alheran da nake son kawowa Najeriya, Jonathan. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara

Idan ba a manta ba, tsohon shugaban kasa Jonathan ya sha caccaka, kushe da hantara kafin zabe, saboda zarginsa na barin masu cin hanci da rashawa suna cin karensu babu babbaka, matsalolin tsaro da kuma sauke wasu manyan masu daraja daga kujerunsu.

Kamar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sunusi Lamido Sunusi, tsohon shugaban sojin kasa, Janar Azubuike Ihejirika, da sauransu.

Ya yi wannan maganar ne a Abuja, lokacin da ake kaddamar da wani littafi a kansa 'Dear President Goodluck Jonathan', wanda tsohon ma'aikacin Daily Times, Bonaventure Melah ya rubuta musamman don girmama shi.

Jonathan ya ce babu wani shugaba na siyasa mai bukatar mulki a lokacin, da ya bashi uzuri. Ya fuskanci caccaka, zagi har da tozarci daga mutane da dama a lokacin.

Jonathan ya kara da cewa, "Idan kana so ka gane wanene shugaba, sai ka duba yanayin shugabancinsa. Nayi matukar burin canja Najeriya ta hanyar ilimi. Shiyasa na shiga batun Almajirai, saboda ya kamata mu kawar musu da jahilci."

KU KARANTA: Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire

Kuma ya ce duk wadanda ya sauke daga mukamansu, yana da dalilai masu karfi da suka sa yayi hakan, amma kowa da irin fassarar da yake masa a lokacin.

A wani labari na daban, amintattun 'yan siyasar Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, sun kai wa Lamidi Adeyemi, Alaafin din Oyo ziyara a ranar Litinin.

Dayo Adeyeye, tsohon ministan ayyuka shine ya jagoranci ziyarar, kungiyar, inda suka ce sunje fadar ne don samun hadin kai don marawa Tinubu baya wurin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Soji Akanni, tsohon sanatan jihar Oyo; Rotimi Makinde, tsohon dan majalisar wakilai; Oyetunde Oko, mijin diyar Bola Tinubu, duk suna cikin wadanda suka kai ziyara fadar Saliu Adetunji, Olubadan din Ibadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel