UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni

UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni

- Majalisar dinkin duniya ta yi ala wadai da harin da 'yan bindiga suka kaiwa daliban jihar Katsina

- Ta bukaci hukumomin Najeriya da su yi gaggawar ceto yaran daga hannun 'yan ta'addan

- Ta yi wannan rokon ne a ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020, inda ta nuna takaicinta a kan lamarin

UN ta yi kira a kan gaggawar sakin daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina a ranar 14 ga watan Disamban 2020, Channels TV ta wallafa.

UN ta nuna takaicin ta ne dangane da satar daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, bayan 'yan bindiga sun kai farmaki makarantar.

Majalisar dinkin duniya ta yi wannan kiran a wata takardar da kakakin babban sakataren, Stephanie Dujarric, ya saki a ranar Litinin.

UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni
UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi

"Babban sakataren UN ya yi ala wadai da harin da 'yan bindiga suka kai wa wata makarantar sakandare a jihar Katsina a ranar 11 ga watan Disamba, a Najeriya, da kuma satar daruruwan daliban makarantar.

"Babban sakataren ya bukaci a yi gaggawar sakin yaran don su samu su koma wurin iyayensu. Ya ce harin ya sabawa dokar kare hakkin bil'adama. Ya roki hukumomin Najeriya da su yi gaggawar kwatar yaran kuma su yi musu adalci," kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'

A wani labari na daban, a ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020, wani Bello Inua Anka ya wallafa hotunan wasu sojoji a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

Kamar yadda ya wallafa, an ga sojojin Najeriya suna gadi da kuma taimakon manoman Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno, yayin da suke girbin shukokinsu a kauyen Koshebe.

Wannan al'amarin yazo ne bayan wasu makonni da 'yan Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa na Zabarmari da ke kauyen Koshebe a karamar hukumar Mafa, yankan rago. Hakan ya janyo mutuwar a kalla manoma 43 dake aiki a gonar shinkafar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel