Rashin tsaro: Farfesa ya bukaci gwamnati da ta diba mafarauta aikin tsaro
- Shugaban Kaduna State Polytechnic, Farfesa Idris Bugaje, ya bayar da shawara a kan yadda za a kawo karshen ta'addanci a Najeriya
- A shawarar da ya bayar, ya ce yakamata gwamnati ta horar da mafarauta 100 a kowacce karamar hukuma a arewa
- A cewarsa, horarwar da za a basu ta zama a kan harkokin sadarwa sannan kuma a tabbatar da ingancin dabi'unsu tukunna
Shugaban Kaduna State Polytechnic, Farfesa Idris Bugaje ya bukaci a horar da mafarautan gargajiya da dama a kowacce karamar hukuma da ke jihohin arewa don ragargazar 'yan boko Haram a arewa maso gabas da kuma 'yan ta'addan da ke addabar arewa maso yamma da sauran yankin a fadin kasar nan.
Kamar yadda yace, ya kamata a horar da mafarauta a kan sadarwa da kuma amfani da dabaru na musamman wurin yakar 'yan ta'adda, daga nan kuma a basu makamai don su ji dadin aiwatar da ayyukan yadda ya kamata.
Kamar yadda ya fadi a wata takarda mai taken "Formula-100: Hanyar magance ta'addanci da rashin tsaro a arewa", Farfesan Engineering din ya ce idan aka horar da a kalla mafarauta 100 a kowacce karamar hukuma a jihohin arewa za su yaka 'yan ta'adda, kuma hakan zai kawo karshen rashin tsaron da ke addabar arewa.
KU KARANTA: Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi
Kamar yadda Farfesa Bugaje ya ce, "Ya kamata a tantance ingancinsu da kyawawan dabi'unsu ta hanyar shugabannin iyalansu, limaman unguwanni da shugabannin kauyakun su."
"Mun dade muna kyale wadannan mafarautan gargajiyar kuma wasu daga cikinsu sun hada kai da 'yan ta'adda," cewar farfesa Bugaje.
KU KARANTA: Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'
A wani labari na daban, a ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020, wani Bello Inua Anka ya wallafa hotunan wasu sojoji a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.
Kamar yadda ya wallafa, an ga sojojin Najeriya suna gadi da kuma taimakon manoman Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno, yayin da suke girbin shukokinsu a kauyen Koshebe.
Wannan al'amarin yazo ne bayan wasu makonni da 'yan Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa na Zabarmari da ke kauyen Koshebe a karamar hukumar Mafa, yankan rago. Hakan ya janyo mutuwar a kalla manoma 43 dake aiki a gonar shinkafar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://facebook.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng