Hotunan sojin Najeriya suna tsaro da taya manoman Zabarmari girbi a gona
- Hotunan sojojin Najeriya suna gadi da taimakon manoman Zabarmari ya karade kafafen sada zumunta
- Wani Bello Inua Anka, ya wallafa hotunan a ranar Juma'a, inda mutane suka yi ta yaba wa kokari da dagewar sojojin
- Sai dai wasu suna ganin maimakon sojojin su yi gadin manoman, kamata yayi su nemi 'yan ta'addan su kashesu
A ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020, wani Bello Inua Anka ya wallafa hotunan wasu sojoji a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.
Kamar yadda ya wallafa, an ga sojojin Najeriya suna gadi da kuma taimakon manoman Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno, yayin da suke girbin shukokinsu a kauyen Koshebe.
Wannan al'amarin yazo ne bayan wasu makonni da 'yan Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa na Zabarmari da ke kauyen Koshebe a karamar hukumar Mafa, yankan rago. Hakan ya janyo mutuwar a kalla manoma 43 dake aiki a gonar shinkafar.
KU KARANTA: Matashi ya bayyana yadda abokinsa yayi wuff da budurwarsa bayan ya yi mata alfarma
Yayin da mutane da dama suka yi ta yaba wa sojojin bisa kokarinsu, wasu kuma gani suke yi hakan bai dace ba.
Wata Hadiza Suleiman ta yi tsokaci a kasan wallafar, inda tace; "Sun kyauta, amma ba haka ya kamata ba.
"Ba zaman gadi ya kamata su yi ba kawai. Abinda ya dace shine su bincika kuma su nemi 'yan ta'addan, ba wai su tsaya jira har sai sun kawo musu farmaki ba.
"A kasar Amurka, ana yin amfani da kwakwalwa da dabara ta musamman wurin bayar da kariya ga ko da mutum daya ne a kasarsu, ina fatan za a fara hakan a Najeriya."
KU KARANTA: Matashi ya bayyana yadda abokinsa yayi wuff da budurwarsa bayan ya yi mata alfarma
A wani labari na daban, Prince Uche Secondus, Shugaban jam'iyyar PDP na Najeriya ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar.
Sauran jiga-jigan jam'iyyar masu ra'ayin tsayawa takarar za su iya yakin neman tikitin, kamar yadda shugaban jam'iyyar yace, The Nation ta wallafa.
Secondus ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari a kan kin amsa gayyatar majalisar tarayya, wacce ta bukaci yayi magana a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng