Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'

Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'

- Mutane da dama sun caccaki gwamnati a kan ikirarin ma'aikatar sadarwa ta rage 50% daga kudin data

- Ma'aikatar ta ce tayi ikirarin rage farashin data tun watan Janairun 2020 zuwa watan Nuwamba, hakan ya janyo cece-kuce

- Masu amfani da data, da kuma siyarwa daga jihohi daban-daban, duk sun musanta inda sukace basu ga wani canji ba

Duk wani mai amfani da data a fadin kasar nan ya caccaki gwamnatin tarayya a kan ikirarin rage kudin data da 50%, Daily Trust ta wallafa.

Wata takarda, wacce ministan sadarwa, Dr Isa Ibrahim Pantami ya sanya hannu, yace an rage kudaden siyan data da 50% tun watan Janairun 2020, inda yace maimakon sayar da 1GB a N1000, ya koma N487.18.

Pantami ya ce ma'aikatar NCC ta samar wa wadanda suke sayar da data wannan rangwamen.

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Najeriya na daya daga cikin zakakuran soji a Afrika, Magashi

Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'
Ba mu gani a kasa ba, 'Yan Najeriya sun caccaki Pantami a kan ikirarin rage kudin 'data'. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Kamar yadda takardar tazo bisa rahoton da NCC ta kaiwa mai girma ministan sadarwa, takardar da mataimakinsa na musamman, Mr Femi Adeluyi, ya fitar.

Sai dai mutane da dama sun musanta wannan ikirarin, inda suka ce basu lura da wani canji ba wurin siyan data.

Wani Deji Eluobomi, daya daga cikin masu siyan data a jihar Osun, ya musanta wannan ikirari, inda yace ba gaskiya bane don ko jiya da safe ya siya data 1GB a N1000.

Wani Eluobomi ya ce "Kila ba a fara bin tsarin ba har yanzu, don ko yau da safe N1000 na siya 1GB."

Wani Muyiwa Ayinde Kareem daga Legas, ya musanta ragin 50% na kudin data, inda yace idan da gaske ne, shine mutum na farko da ya kamata ya sani don yana amfani da data kuma yana siyarwa.

Muktar Abdullahi daga Kano, ya ce bai ga wani ragi ba a batun siyar da data.

KU KARANTA: Ba mu gayyaci Buhari don kure shi ba, Kakakin majalisar wakilai

A wani labari na daban, Prince Uche Secondus, Shugaban jam'iyyar PDP na Najeriya ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar.

Sauran jiga-jigan jam'iyyar masu ra'ayin tsayawa takarar za su iya yakin neman tikitin, kamar yadda shugaban jam'iyyar yace, The Nation ta wallafa.

Secondus ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari a kan kin amsa gayyatar majalisar tarayya, wacce ta bukaci yayi magana a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel