Yadda ma'aikaci a ma'aikatar man fetur ya bai wa kansa kwangilar N145m
- Majalisar dattawa ta tuhumi ma'aikatar man fetur a kan biyan wani ma'aikacinta N145,000,000
- Zunzurutun kudin da ma'aikatar ta shaka masa musamman don tallace-tallace da yada labaran ma'aikatar
- Majalisar ta bukaci ma'aikatar da tayi gaggawar maida wa gwamnatin tarayya kudaden cikin asusunta
Majalisar dattawa tana tuhumar ma'aikatar man fetur a kan bai wa wani ma'aikacinta N145,000,000, Daily Trust ta wallafa.
Korafin yana cikin wata takarda ta Odita janar na gwamnatin tarayya a 2015, wacce kwamitin majalisar dattawa na asusun gwamnati ta amsa.
Kwamitin, wanda Sanata Matthew Urhoghide yake shugabanta, ta yi bincike a kan kudaden da ma'aikatun gwamnatin tarayya suke kashewa.
Wakilin sakataren ma'aikatar, Godwin Akubo, shine ya bayyana gaban kwamitin don kare ma'aikatar daga zargin da ake mata.
KU KARANTA: Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi
KU KARANTA: Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa
Kamar yadda takardar tazo: "MTB ta amince da bayar da N145,000,000, kuma ta biya wani ma'aikacinta don tallace-tallace na gidajen talabijin da jaridu na tallar PIB, maimakon a bai wa kwararrun kuma masana harkar damar baje gwanintarsu don a tabbatar da wanda ya cancanci kwangilar."
A lokacin da Akubo yake kare ma'aikatar, ya ce ma'aikacin da suka bai wa kwangilar, wanda dama ya saba da harkokin yada labarai, ya dade a kan irin harkar.
"Shine jagaba wurin yada labaran ma'aikatar da kuma jaridu da gidajen talabijin. Yana da mutukar hanzari da kuma dagiya wurin yada labarai cikin sauri, shiyasa ma'aikatar ta bukaci yin aiki dashi, don hakan zai bunkasa ta."
Sai dai, Akubo ya gaza bayar da bayani a kan takardu da sauran alamu da suka tabbatar da biyan N145,000,000 a matsayin kudin yada labarai, hakan ya fusata 'yan majalisar.
Sanata Urhoghide ya bukaci su yi gaggawar mayar wa da gwamnatin tarayya N145,000,000 cikin asusunta.
A wani labari na daban, kamar yadda Mail Online ta ruwaito, wanda ake zargin, manajan wata makaranta, ya kashe £4,100,000 a kan mata 4, ciki har da matarsa da karuwansa.
Ya fara aiki a Haberdasher, wacce take da jibi da makarantun gwamnati masu irin sunanta a 1997, The Cable ta wallafa.
Thacker ya ce a 2006, Kayode ya fara amfani da tsarin tura kudi na BACS wurin hankada wa matarsa Grace kudade, zuwa asusunta. Daga nan ya koma kashe £98,000 duk wata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng