Kada ku haifar da rudani tsakanin gwamnoni, Wike ya gargadi PDP

Kada ku haifar da rudani tsakanin gwamnoni, Wike ya gargadi PDP

- Nyesome Wike, gwamnan Jihar Rivers ya yi ikirarin cewa Kwamitin Gudanarwa na PDP na neman janyo rudani a jam'iyyar tsakanin gwamnoni

- Ya kuma gargadi Shugaba Muhammadu Buhari a kan rashin amsa gayyatar da Majalisar Wakilai tayi masa game da kallubalen tsaro a kasar

- Wike ya kuma shawarci jam'iyyarsa ta PDP ta yi amfani da damar da ta ke da shi don kwace mulki daga hannun APC da ya ce ta gaza

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya zargi Kwamitin Gudanarwa (NWC) ta jam'iyyar PDP da kitsa mugun ƙulli tsakanin gwamnonin PDP da kuma jefa jam'iyya cikin haɗarin wajen ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan a babban zaɓen 2023.

Ya kuma gargaɗi Shugaba Muhammad Buhari akan irin kallon da ƴan Najeriya wanda suka bashi amana zasu yi masa matuƙar ya gaza karrama gayyatar da Majalisar Wakilai don bayani akan makomar tsaro a faɗinn ƙasa.

Wike ya bayyana hakan yayin wata hirar kaitsaye a shirin gidan talabijin a Port Hacourt inda yace abin takaici ne ace maimakon jam'iyyar tayi tayi amfani da shekaru biyar da ta APC ta shafe ta na wasa da hankalin jama'a da mulkin karya wajen gyara miyar da,sai kwamitin NWC na PDP ya ɓuge da wargaza jam'iyyar PDP.

Kada ku haifar da rudani tsakanin gwamnoni, Wike ya gargadi PDP
Kada ku haifar da rudani tsakanin gwamnoni, Wike ya gargadi PDP. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

KU KARANTA: Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi

"Ya kamata ace PDP ta girbi romon gazawar jam'iyyar APC. A zahirance abin da ya kamata jam'iyyar adawa ta yi kenan. Idan ka tambayi shin ƴan Najeriya suna jiran canji ne? Eh. Idan ka tambayeni a matsayin ɗan jam'iyyar PDP, a shirye na ke na goyi bayan jam'iyyata ta PDP ta karɓi mulkin ƙasar nan, eh."

"Amma idan ka tambayeni a halin yanzu da ake ciki yanzu, shin shugabancin jam'iyyar PDP na da niyyar sharɓar romon damar gazawar APC don kawo canji, zan ce maka a'a."

Ya yi ƙarin hasken cewa maimakon maida hankalin akan dabarun yadda zasu yi amfani da matsalar jam'iyyar APC don sharewa kansu hanyar mulki ɗoɗar,Kwamitin NWC na faman kitsa mugun ƙulli tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP ta hanyar amfani da tsofaffin gwamnoni guda biyu na Jihohin Imo da Cross River da kuma wani Sanata mai ci daga jihar Benue.

"Ya ce jam'iyyar Adawa da ya kamata ace ta haɗe kanta don yin aiki tuƙuru tare,don karɓe al'amuran gwamnati, saboda mutane na jiran wannan damar,amma shugabancin kwamitin NWC ba'a shirye yake ba kwata kwata,abin da yake gabansu shine su kitsa mugun ƙulli tsakanin gwannoni saboda ra'ayin su na son zuciya da son rai. Kuma wannan haɗamar ita zata rusa su."

KU KARANTA: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Gwamnan ya ce saboda bashi da ikon sauye sheƙa zuwa APC ko wata jam'iyya ta daban, zai cigaba da tabbatar da ɗorewar numfashin jam'iyyar PDP.

"Ba zan bari kowa ya kar jam'iyyar PDP ba. Ba zan yi ba sannan ba zan iya komawa Jam'iyyar APC ba. To,dukkan wani wanda yake yunƙurin wargaza PDP, ba zan ƙyale shi ba. Duk wanda na hango yana barazanar zambatar PDO ko neman zame mata barazana bazan ƙyale ba."

Ya bayyana hukuncin da kwamitin NWC ta yanke akan gwamna Samuel Ortom ya jagoranci kwamitin sulhu don sulhunta matsalolin jam'iyya a jihohin Niger da Plateau a matsayin bigi bagiro saboda kawai ra'ayin jam'iyya ya fi karkata kan jihar Niger.

Gwamnan ya zargi shugabancin NWC na yanzu da kawo naƙasu wajen aiwatar da tsarin jam'iyya don ta kasance mai mulki, ko ta lashe zaɓen shekarar 2023.

"Kwamitin NWC na yanzu bai sa ra'ayi ko yunƙurin yin wani kataɓus don karɓar gwamnati a 2023. Idan har burinku shine ku cigaba da kasancewa masu iko,to tabbas baku damu da ku ci zaɓe ba."

Gwamna Wike ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya yi jawabi kan tsantsar rashin tsaro da kashe kashe a jihohin Borno da faɗin ƙasa sannan ya cika alƙawarinsa na karrama gayyatar da Majalisa ta yi masa.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel