Yan ta'adda sun yi awon gaba da Ango da abokinsa bayan daurin aure
- An sake sace ma'aikatan kungiyoyin tallafi a Arewa maso gabashin Najeriya
- Wannan ba shi karo na farko da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suke sace ma'aikatan tallafi ba
- Yayinda suke amsan kudin fansa kan wasu, sun kashe wasu
Yan ta'addan sun yi awon gaba da ma'aikatan tallafi biyu a jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya yayinda suke hanyar dawowa daga daurin aure, majiya daga jami'an tsaro sun bayyana ranar Asabar.
Mutanen da aka sace sun ma'aikacin kungiyar ciyar da al'umma na majalisar dinkin duniya WFP, wanda shine Angon da kuma abokinsa na kungiyar RedCross da ya raka shi.
Majiyoyin sun bayyana cewa yan ta'addan ISWAP ne suka sace su ranar Laraba, kusa da kauyen jakana.
"Yan ta'addan ISWAP sun dauke ma'aikatan tallafi biyu yayinda suka tare hanya kusa da Jakana," wata majiyar UN ta bayyana AFP.
Matasan na hanyar komawa Maiduguri daga jihar Adamawa yayinda aka taresu misalin karfe 1:30 na rana, majiyar ta kara.
Ma'aikacin WFP "ya yi daurin aurensa ranar 28 ga Nuwamba kuma abokin aikinsa na Red Cross ne babban abokin ango," cewar majiya daga majalisar dinkin duniya.
Wata majiya a gidan Soja ta tabbatar da aukuwan lamarin.
KU DUBA: Harin Kankara: Gwamna Masari ya kulle dukkan makarantun kwana a jihar Katsina
KU KARANTA: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar sakamakon zabe
A bangare guda, dan majalisar dokokin jihar Taraba, Bashir Bape, da aka yi garkuwa da shi ya samu yanci a daren Juma'a, majiya daga hukumar yan sanda da iyalansa sun tabbatar.
A cewar rahoton Premium Times, har yanzu ba a san ainihin adadin kudin da aka biya kudin fansa ba amma majiya daga gidan dan majalisan ya bayyana cewa: "an biya kudin fansa kafin aka sakeshi."
"An sake shi a daren jiya misalin karfe 10 na dare, kuma yanzu yana asibiti. Muna godiya ga dukkan wadanda suka taya mu addu'a," ya kara.
Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda a jihar, David Misal, ya tabbatar da lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng