Gayyata zuwa majalisa: Buhari bashi da abiinda zai sanar wa 'yan Najeriya, PDP

Gayyata zuwa majalisa: Buhari bashi da abiinda zai sanar wa 'yan Najeriya, PDP

- A ranar Alhamis, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo

- Jam'iyyar ta ce shekaru 5 kenan Buhari yana mulkin Najeriya amma ya gaza tsinana komai

- Ta ce Buhari ba zai iya fuskantar 'yan majalisar tarayya bane saboda ba zai iya kare kansa ba

Jam'iyyar PDP ta yi wa Buhari kaca-kaca a ranar Alhamis. Ta ce ya kasa tabuka komai cikin shekaru 5 da yake kan karagar mulki, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan yace, Buhari bashi da abinda zai cewa 'yan majalisar tarayya, shiyasa ba zai iya amsa gayyatarsu ba.

A cewarsa, "Shugaban kasa a tsorace yake, bashi da abinda zai fada wa 'yan Najeriya a kan matsalar tsaro. Wannan yasa yake ta kame-kame, ya tsere yaki fuskantar 'yan majalisar. Ya kasa yin komai tun da ya hau mulki, ciki har da bayar da tsaro."

Gayyata zuwa majalisa: Buhari bashi da abiinda zai sanar wa 'yan Najeriya, PDP
Gayyata zuwa majalisa: Buhari bashi da abiinda zai sanar wa 'yan Najeriya, PDP. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa

Kakakin jam'iyyar PDP ya kara da cewa, babu wani shiri da 'yan majalisar tarayya, 'yan jam'iyyar PDP suka yi don tozarta shi a taron yau. Tsoro ne kawai ya kama shugaba Buhari.

Ologbondiyan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ake tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin a Legas.

Dama makon da ya gabata, majalisar tarayya, wacce Femi Gbajabiamila yake jagoranta, ta gayyaci shugaba Buhari don tattaunawa da shi a kan matsalar rashin tsaro, sakamakon kashe-kashen manoman Zabarmari 45 da aka yi a jihar Borno.

KU KARANTA: Buhari ya sanar da gwamnoni hanyar da za su bi wurin magance rashin tsaro

Lauretta Onochie, hadimar Buhari ta harkokin yada labarai ta ce zai bayyana gaban majalisar tarayya a ranar Alhamis. Sai dai labarai sun fara yaduwa a kan cewa ba zai samu damar amsa gayyatar majalisar ba.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Yobe tayi alkawarin bayar da gudunmawa dari bisa dari wurin kawo karshen Boko Haram a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde-Gubana ya yi rokon ne a ranar Laraba a Damaturu, bayan sun kammala wani taro da gwamna Mai Mala-Buni a kan harkokin tsaro.

Ya ce sun yi taron ne don sanin hanyoyin da za a bullo wa tsaro a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel