Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta dauka alwashin ba wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki

Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta dauka alwashin ba wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki

- Gwamnatin jihar Yobe ta roki jami'an tsaro da su mayar da halaccin da gwamnati take yi musu

- Kamar yadda mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde-Gubana yace, suna bukatar hadin kan jami'an tsaro

- A cewarsa, hakan ne zai taimaka wurin kawo karshen ta'addancin 'yan Boko Haram da tabbatar da tsaro

Gwamnatin jihar Yobe tayi alkawarin bayar da gudunmawa dari bisa dari wurin kawo karshen Boko Haram a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde-Gubana ya yi rokon ne a ranar Laraba a Damaturu, bayan sun kammala wani taro da gwamna Mai Mala-Buni a kan harkokin tsaro.

Ya ce sun yi taron ne don sanin hanyoyin da za a bullo wa tsaro a jihar.

KU KARANTA: Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah

Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta dauka alwashin ba wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki
Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta dauka alwashin ba wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Da kafa, magidanci ya taka nisan Abuja zuwa Kano don tserewa matarsa

"Mun yi taron ne don karin haske a kan matsalar tsaro. Musamman yanzu da muke tunkarar lokacin zafi, don 'yan Boko Haram za su fara yawo tsakanin iyakokin Borno, Chadi da kasar Nijar.

"Muna yin iyakar kokarinmu don ganin mun samar da tsaro da zaman lafiya a jiharmu,"a cewarsa.

Barde-Gubana ya roki jami'an tsaro da su mayar da halaccin da gwamnati take yi musu wurin dagewa da nunka kokarinsu don kawo karshen ta'addanci.

A wani labari na daban, a taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni, ya zauna tsaf ya saurari korafi daga yankuna 6 da ke kasar nan, daga bakin gwamnoni, a kan harkokin tsaro da ke addabar kasarnan.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu yace, shugaban kasa ya ce, "Wajibi ne gwamnati tayi aiki tare da shugabannin gargajiya. Ya kamata a hada kai dasu don a san ta inda za a bullo wa lamarin."

Buhari ya ce mulkinsa ya yi kokarin gyara yankunan arewa maso gabas da kudu-kudu, amma yankin kudu-kudu suna cikin mawuyacin hali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel