Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno

- Yan majalisa sun bukaci shugaban kasan ya yi musu bayanin dalilin da ya sa aka gaza shawo kan matsalar tsaro

- Bayan rikici da cece-kuce, Buhari ya amince zai bayyana gabansu kuma zai yi jawabi

- Bayan alkawarin gurfana gaban yan majalisan dokokin tarayya, Buhari ya canza ra'ayinsa

Ya tabbata cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis domin jawabin kan tabarbarewan tsaro a fadin tarayya.

TVCNews ta samu bayani daga bakin mai tsawatarwa a majalisa, Muhammad Munguno cewa shugaban kasan ya canza ra'ayinsa.

Ya ce ana kyautata zaton Buhari ya canza ra'ayinsa na zuwa ne saboda zargin da ake cewa yan majalisan PDP za su ci mutucinsa.

Yan majalisan PDP sun yi ganawar sirri a daren Talata.

KU DUBA: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno Credit: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC

Mun kawo muku cewa bayan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan gurfanar Buhari gaban yan majalisun dokokin tarayya.

A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da 'yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Sannan sun ce za su tayar da wannan maganar a taron NEC da za su yi. Gwamnan jihar Ondo, Mr. Akeredolu, ya nuna amincewarsa a kan wannan batun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng