Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

- Manyan masana, tsaffin ma'aikatan gwamnati, da sauraunsu, sun bayyana bacin ransu kan yadda ake jagorantar Najeriya

- Sun yi kira ga yan Najeriya su mike tsaye domin kwato kasarsu daga hannun shugabannin dake ci

- Daga cikinsu akwai Malamin addini, John Cardinal da babban Malami Attahiru Jega

Wasu manyan masu fada aji a Najeriya sun yi ittifakin cewa Najeriya ta zama kamar mota maras matuki kuma duk mota mara mai juyata hadari za tayi.

Wadannan mutanen sun hada da babban faston katolikan, John Cardinal Onaiyekan; tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega; Dr Hakeem Baba Ahmed da Janar Martin Luther Agwai (mai murabus)

Sauran sune Jibrin Ibrahim, Dr. Nguyan Shaku Feese, Dr. Usman Bugaje, Adagbo Onoja, Amb. Fatima Balla, Ambassador Zango Abdu, Auwal Musa Rafsanjani, da Chris Kwaja.

Hakazalika akwai Dr. Hussaini Abdu, Kemi Okenyodo, Jim Gala, Aisha Muhammed Oyebode da Tsema Yvonne

Sun bayyana hakan a jawabin da suka saki ranar Alhamis karkashin kungiyar aiki domin samar da zaman lafiya da shugabanci (NWGPG).

Sun yi ikirarin cewa sune wadanda suke son ganin Najeriya ta gyaru.

A cewarsu, Najeriya ba tada wani shugabanci na kwarai, kawai tuka kanta take yi.

"Sakamakon haka shine rashawan da ta wuce gona da iri, gashi kuma ana kokarin kashe hukumomin yaki da rashawan, yayinda aka rage gurfanar da barayi kuma suna kara yawa." Suka ce.

DUBA NAN: Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya
Credit: Onaiyekan
Asali: Facebook

Sun ce lokaci ya yi da ya kamata mutanen Najeriya su tashi tsaye, su daina korafi da surutai, su hada kansu.

A cewarsu, rashin tsaro na karuwa kulli yaumin kuma babu wani takamammen shirin da ake yi na shawo kan matsalar .

Hakazalika sun yi gargadin cewa mutane sun fara fidda rai daga kasar nan kuma hakan ya sabbaba kiraye-kirayen ballewa da wasu sassa ke yi.

DUBA NAN: An yi zaman majalisar Sarki na farko karkashin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (Hotuna)

A bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu jihar da ta kai jiharsa yaki da rashawa a Najeriya saboda jihar kadai ke da hukumar mai karfi a gaba daya kasar mai kokari.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron murnar ranar Ombudsman da akayi a makarantar yaki da rashawa (KANCI) a Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel