2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje

2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje

- Duk da yadda shekarar 2020 tazo cikin talauci da tsanani, amma akwai wadanda suka caba a cikinta

- Wasu fitattun mutane sun gwangwaje iyayensu da kyautuka na ban mamaki kamar motoci da gidaje

- Sanannun 'yan Najeriyan, sun wallafa hotuna da bidiyoyin kyautukan, inda aka ga yadda iyayen suka cika da farinciki

Duk da yadda shekarar 2020 tazo cikin tashin hankali da rikici, amma har yanzu akwai wadanda suke walwala, suna siyan abubuwa ga kansu da iyayensu.

Akwai wasu sanannu 'yan Najeriya da suka siyawa iyayensu motoci, wasu kuma suka gina musu gidaje.

Kafar sada zumuntar zamani ta Instagram ta bayar da gudunmawa sosai, inda suka bayyana samunsu, kuma duniya ta gani.

2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje
2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje. Hoto daga @officialemmanuela/@nina_ivy/@alexekubo
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bayan kama budurwarsa tana cin amanarsa, saurayi ya bukaci shawara a kan abinda ya dace da ita

Ana tsaka da talauci, sakamakon cutar COVID-19 ga jarumai da sanannun mutane wadanda suka gwangwaje iyayensu da kayan alatu.

1. Jarumin fina-finan Nollywood, Alex Ekubo

Jarumin nan ya gwangwaje mahaifiyarsa da dalleliyar mota. Ya wallafa hotuna da bidiyon da suka nuna yadda mahaifiyarsa ta shiga cikin matsanancin farinciki a shafinsa na Instagram.

2. DJ Kaywise

Sanannan saurayin ya siya wa mahaifiyarsa kasaitacciyar mota sabuwa dal. Ya siya mata ne a matsayin kyautarsa a gareta ranar zagayowar haihuwarta.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina

3. Nina wacce tayi fice a BBNaija

Budurwar wacce take zaune a Amurka, ta siyawa mahaifiyarta katuwar mota a ranar da ta cika shekara 60 a duniya.

4. Jarumar fina-finan Nollywood, Eve Esin

Duk da mahaifiyarta ta rasu, hakan bai hanata kyautar gida a bakacin mahaifiyarta ba. Inda tace ta sadaukar da gidan ga mahaifiyarta.

5. Jarumar fina-finan Nollywood, Bimbo Afolayan

Bayan kwanaki kadan da wani mai gida ya wulakanta iyayenta, kuma al'amarin ya karade kafafen sada zumuntar zamani. Ta share musu hawaye, inda ta gwangwaje su da katafaren gida.

6. DJ JMasta

Bayan ya zage da yiwa mawaki Phyno aiki, ya samu ya gina wa iyayensa gida, bayan yin shekaru yana ayyuka tukuru. Ya bayyana yadda mutane sukayita zundensa akan karamin aikin da yakeyi.

7. Dan wasan kwallon kafa, Henry Onyekuru

Dan kwallon ya wallafa hotunan makadeden gidan da ya gina wa mahaifiyarsa, ana tsaka da annobar Coronavirus.

8. Mai bidiyon ban dariya, Emmanuella

Yarinyar mai shekaru 10 ta wallafa hotunan gidan da ta gina wa mahaifiyarta. Emmanuella ta lashi takobin gina wa mahaifiyarta gidan da yafi wannan kyau.

A wani labari na daban, wani magidanci dan kasar Italiya mai suna Forrest Grump an tsince shi yana tsaka da tafiya a yankin Adriatic coast da ke kasar Italiya, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ya bar gidansa da ke Como a makon da ya gabata kafin 'yan sandan da ke Fano su tsare shi.

An zarge shi da karya dokar kullen korona tare da sanya masa haraji. An gano cewa fada yayi da matarsa shine yasa ya fara tattakin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng