Bayan kama budurwarsa tana cin amanarsa, saurayi ya bukaci shawara a kan abinda ya dace da ita
- Yaudara a soyayya tana da radadi, musamman idan ka amince da mutum dari bisa dari
- Wani saurayi, ya wallafa hoton budurwarsa tare da wani saurayi suna shakatawa
- Saurayin ya bukaci abokansa na shafin Twitter su bashi shawarar yadda zai bullo wa lamarin
Yaudara a soyayya tana da zafi musamman idan wanda ka yarda dashi ne. Wani saurayi ya wallafa labarin yadda budurwarsa ta ha'ince shi a fili, har ta wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Soak_ZA ya ce budurwarsa ta wallafa hotonta tare da wani saurayi, wanda ya kwantar da kansa a cinyarta.
Bayan ya wallafa hoton sai yayi tsokaci a karkashin hoton, inda yace, "'Yan uwa, ban sani ko ina zakewa a kishi bane. Amma idan kai ne budurwarka ta wallafa wannan a shafinta, ya za ka ji? Menene abu na farko da zai zo zuciyarka? Ku taimaka kada ku share ni."
Bayan nan ne mutane suka yi ta yin tsokaci a karkashin wallafar.
Wani asanda_tee ya ce: "Bai dace ka yi wani abu ba. Ka kyaleta kawai."
OpokuHlengiwe ya ce: "Kada ka makale mata, kada ka tambayeta dalilinta na aiwatar da hakan. Ina ga karshen wulakancin da budurwa za ta yi wa saurayinta kenan."
UmalambaneZN ya ce: "Ganinta tare da wani yana nuna ba ta tare da kai."
KU KARANTA: Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000
KU KARANTA: Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu
A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Bayelsa, sun kama wata Eniye Zuokemefa Peter, bisa zargin kashe mijinta, Enebraye Zuokemefa Peter, wanda malami ne a kwalejin ilimin jihar Bayelsa, da ke Sagbama a kwanakin karshen mako.
An kama Mrs Peter ne a kan korafin da 'yan uwan mamacin suka gabatar wa hukuma a kan yunkurin kashe shi da tayi.
Dama ta zarge shi da rashin kamun kai saboda ta samu labarin ya haifi yara 2 da wata mata ba tare da aure ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng