Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya

Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya

- An daura auren wasu masoya a cibiyar killace masu cutar coronavirus bayan an auna amaryar an gano tana da cutar

- Ana saura sa'o'i kadan a daura auren, sakamakon gwajin da amaryar tayi ya bayyana cewa tana dauke da cutar

- Bayan angonta ya ga ba zai iya hakura ba ya bukaci a daura musu aurensu, Allah bar shi daga baya sai su tare

An daura auren wasu masoya 'yan kasar Indiya a cibiyar killace masu cutar COVID-19, bayan an auna amaryar an gane tana da cutar ana saura sa'o'i kadan a daura aurensu.

Kamar yadda hotuna suka gabata, ma'auratan suna sanye da abubuwan kariya daga cutar, yayin da suke tsaye a harabar cibiyar da ke Baran, yammacin Rajasthan, kamar yadda Daily Star ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito yadda malamin majami'ar da ya daura musu aure ya sanya rigar kare kai daga mummunar cutar.

Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya
Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya. Hoto daga www.Reuters.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa

Kamar yadda wata ma'aikaciyar lafiya mai suna Rajeedra Meena tace, an kwantar da amaryar a cibiyar killace masu cutar bayan an aunata da wani dan uwanta, inda aka gane suna dauke da cutar COVID-19.

Rajendra ta ce: "Sai da muka tuntubi iyayensu, kuma suka amince a daura auren a cibiyar killace masu cutar ba tare da aiwatar da wani shagali na gargajiya ba."

KU KARANTA: Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa

A wani labari na daban, wata mata ta maka saurayinta a kotu sakamakon bata mata lokaci duk da shekarunsu 8 tare amma ya gaza aurenta.

Ngoma ta sanar da wata kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekaru 28, wanda yayi mata alkawarin aure.

A cewar Mwebantu, har yanzu Ngoma tana zaune da iyayenta duk da ta haifa wa Herbert da guda daya, shi kuma yana zaman kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng