FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu

FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa fiye da mutum dubu talatin da takwas sun nuna sha'awar son zama 'yan Nigeria

- Dakta Shuaib Begore, babban sakatare a ma'aikatar harkokin cikin gida, ya sanar da hakan a Abuja

- Matasa daga Nigeria kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen duniya musamman turai

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta sanar da cewa jimillar mutane 38,051 'yan kasashen ketare ne suka mika takardar nuna sha'awar zama 'yan Nigeria daga watan Satumba na shekarar 2018 zuwa watan na shekarar 2020.

Babban sakataren ma'aikatar harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Belgore, ne ya fadi hakan yayin wani taro a Abuja, kamar yadda tribune ta rawaito.

Ta bayyana cewa ma'aikatarsu ta samu takardun masana'antu 45,751 da ke son matsaguni da Kuma mutane 38,051 da ke son gwamnati ta sahale musu su zama 'yan Nigeria.

DUBA WANNAN: Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba za mu taba yin sulhu ba

FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu
FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu @Premiumtimes
Source: Twitter

Dumbin matasa daga Nigeria da sauran kasashen nahiyar Afrika kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen ketare, musamman Turai da sauran wasu kasashe da suka samu cigaba.

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta ɗage zamanta da kungiyar ASUU

Legit.ng ta rawaito gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, na cewa duk da kisan manoma 43 da sauran kashe-kashe da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel