Babu dan Najeriyan da ya kamata ya mallaki fiye layukan waya 3 - Pantami

Babu dan Najeriyan da ya kamata ya mallaki fiye layukan waya 3 - Pantami

Ministan sadarwa, Dakta Isa ali Pantami, ya umurci hukumar sadarwan Najeriya NCC ta tabbatar da cewa kada kowani dan Najeriya ya mallaki fiye da layukan waya 3.

Ministan ya bada umurnin ne a ranar Laraba a jawabin da hadimin, Dakta Femi Adeluyi, ya rattaba hannu inda ya umurci NCC ta sake duba dokar rijistan layukan waya.

Jawabin ya kara da cewa akwai bukatan hakan ne bisa ga rahoton da aka samu daga hukumomin tsaro, bayan samun nasarar kawar layukan da ba'ayi rijista ba a Satumban 2019.

Babu dan Najeriyan da ya kamata ya mallaki fiye layukan waya 3 - Pantami
Babu dan Najeriyan da ya kamata ya mallaki fiye layukan waya 3 - Pantami
Asali: UGC

Ministan ya kara cewa hukumar NCC ta tabbatar da cewa sai mutum ya mallaki lamban zama dan kasa NIN kafin ya iya rijistan layi. Wadanda kuma ba yan kasa ba, a yi amfani da bizansu.

A cewarsa, a tabbatar da kowani dan Najeriya ya bayar da lambar zama dan kasa NIN na da 1 ga watan Disamba, 2020.

Yace: "A tabbatar da cewa masu sayar da layukan waya na iya yiwa mutane rijista, sabanin yin rijistan layukan da kansu kafin sayarwa."

"A samar da iyakan layukan wayan da kowani mutum zai iya mallaka, misali guda 3 akasari."

"A tabbatar da cewa babu layi mara rijista mai aiki."

Mun kawo muku rahoton cewa Dakta Isa Ali Pantami ya sanar da cewa tabbatar da tsarin Integrated Payroll and Personel Information System (IPPIS) ya sa an bankado ma'aikatan bogi har 6,000 a gwamnatin tarayya.

Pantami ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye dalibai karo na 29 a jami'ar fasaha da ke Minna a jihar Neja, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ministan, wanda ya bayyana manufar gwamnatin tarayya na hana ci gaban rashawa a Najeriya, ya kara bayyana cewa gwamnatin tarayya ta adana naira biliyan 24 tun bayan da ta tabbatar da asusun bai daya (TSA) a kasar nan.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta kirkiro da tsarin IPPIS da TSA don kawo karshen rashawa a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel