Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa

Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa

- Wani David mai shekaru 27 ya daki karuwarsa, wacce ta haifa masa diya mace har ta kai ga mutuwa

- Kamar yadda makwabta suka tabbatar, sun ji ihunta da misalin 11:30 na dare, yayin da yake bugunta

- Al'amarin ya faru a jihar Bayelsa a ranar Lahadi da daddare, inda ya rufe kofa ya cigaba da kirbarta

Wani Promise David mai shekaru 27 yayi wa karuwarsa, Esther Pascal, mai shekaru 18 dukan kawo wuka har ta kai ga mutuwa sakamakon fada a kan abinci da kudin kulawa da diyarsa.

Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi da tsakar dare a layin Ebis Machanic, Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Marigayiyar ta haifa wa mutumin mai aiki a wani wurin wanke mota, yarinya wacce yanzu shekarunta 2 da haihuwa, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa

Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa
Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa. Hoto daga @thenation
Source: Twitter

Wasu makwabtansu sun ce fadan tsakanin masoyan ya dade yana faruwa. Sun ce sun farka da misalin 11:30pm na ranar Lahadi, sakamakon jin ihun matar tana neman taimako.

A cewar shaidar: "Lokacin da muka isa bakin kofar, sai muka fahimci an kulle kofar ta cikin dakin. Sai da muka balla kofar tukunna muka ga matar a kasa.

"Mun yi kokarin debo ruwa don mu yayyafa mata, ashe ba suma tayi ba, mutuwa tayi. Take a nan muka kira 'yan sanda muka sanar da su da abinda ya faru."

KU KARANTA: Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27

Wasu daga cikin ganau din, sun ce mutumin ya buga mata wani abu mai nauyi a kanta, wasu kuma suka ce naushinta yayi a kai.

Yanzu haka wasu 'yan kungiyar GRI wacce matar gwamnan Bayelsa ta kirkira, Mrs. Gloria Diri, sun je wurin da abin ya faru.

Dise Sheila Ogbise, wata lauya, wacce ita ce mataimakiyar shugaban GRI ta ce al'amarin ya kazanta, kuma ta yi kira a kan bukatar yadda za a kawo karshen zaluncin mata a gidajensu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda a ofishinsu dake Ekeki ana cigaba da bincike.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike, sun samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a sansaninsu da ke wuraren dajin Kuduru dake jihar Kaduna a ranar Asabar.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda, inda yace rundunar ta yi amfani da dabara ta musamman wurin kai hari ga 'yan ta'addan.

Fiye da 'yan bindiga 10 sojojin suka kashe a dajin, inda suka yi amfani da ISR wurin gano maboyar tasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel