Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)

- Rundunar sojoji ta Operation Whirl Stroke tana samun nasarar ragargazar 'yan ta'adda

- A ranar Lahadi, 6 ga watan Disamban 2020, sun kashe 'yan ta'adda 3 tare da kwace makamansu

- Hakan ya faru ne a kauyen Tsehombe-Adaka bayan 'yan sa kai sun sanar da sojoji inda 'yan ta'addan suke

A jiya, ranar 6 ga watan Disamba ne rundunar Operation Whirl Stroke ta amsa kiran 'yan sa kai a kan wani hari da ake zargin wasu makiyaya na kauyen Tsehombe-Adaka suka kai.

Take a nan aka yi karon batta tsakanin 'yan ta'addan masu miyagun makamai da kuma jaruman sojojin.

Sojojin sun zagaye 'yan ta'addan, inda suka yi kaca-kace da su har suna kashe mutane 3 a cikinsu. Sauran kuma suka tsere da raunuka sakamakon harbin da suka sha.

Rundunar ta samu nasarar amsar bindiga kirar AK-47 da magazine daya mai rounds 5 ta 7.62mm Special ammunition.

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)
Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna). Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Rundunar ta cigaba da yin sintiri don gudun kada 'yan ta'adda su mamayesu, sannan a shirye take da su ga sun ragargaji duk wani dan ta'adda da zai kai wa yankin farmaki.

Mutanen yankin sun roki sojojin da su cigaba da ayyukansu, sannan sun lashi takobin sanar da su duk wani labari da suka samu a kan 'yan ta'addan.

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)
Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna). Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)
Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna). Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta amince wa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ake zargin damfarar naira biliyan 2.2, ya tafi kasar waje neman lafiya.

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya amince da bukatar da lauyansa, Ola Olanipekun (SAN), wanda ya bukaci kotu ta amince yayi tafiyar.

EFCC, ta lauyanta Rotimi Jacobs (SAN), bai kalubalanci bukatar Fayose ba, Channels TV ta wallafa hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel