Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000

Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000

- Wani saurayi dan Najeriya ya sha caccaka a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan ya bayar da wata gurguwar shawara

- Ya ce tsaf mutum zai iya aure matsawar yana daukar albashin da ya kai N30,000 duk wata, ya ce matsawar mutum yana maneji

- Ya bayar da misalin yadda wani mutum mai daukar N15,000 duk wata, kuma yana da yara 8, suke rayuwa cikin kwanciyar hankali

Wani dan Najeriya ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wanda ya janyo cece-kuce.

Mutumin ya ce mutum zai iya yin aure idan yana samun N30,000. A cewarsa, matukar mutum yana maneji tsaf zai iya tafiyar da rayuwar iyalinsa lafiya da albashin N32,000 duk wata.

Kamar yadda ya wallafa: "Idan kana samun N30,000 duk wata, za ka iya yin aure. Na san wani mutum mai iyali, sun kai mutane 8, inda mijin yake daukar albashin N15,000, matar kuma N7,000 sannan diyarsu ta farko N10,000.

"Suna zaune cikin kwanciyar hankali. Idan za su iya hakan, kai ma za ka iya. Maneji da rayuwa kawai za ka yi."

KU KARANTA: Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa

Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000
Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000. Hoto daga @Mazimum
Asali: Twitter

Mutane da dama sun yi ta tsokaci iri-iri a karkashin wannan wallafar tasa.

Wani Prince of Jakarta cewa yayi, "Mutumin nan ya baku gurguwar shawara. Ta yaya za'a yi mutum mai daukar N30,000 a duk wata ya iya daukar dawainiyar iyalinsa?"

Wani Matthew cewa yayi "Ba zai taba yuwuwa ba musamman a nan Kenya."

KU KARANTA: Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27

A wani labari na daban, a jiya, ranar 6 ga watan Disamba ne rundunar Operation Whirl Stroke ta amsa kiran 'yan sa kai a kan wani hari da ake zargin wasu makiyaya na kauyen Tsehombe-Adaka suka kai.

Take a nan aka yi karon batta tsakanin 'yan ta'addan masu miyagun makamai da kuma jaruman sojojin.

Sojojin sun zagaye 'yan ta'addan, inda suka yi kaca-kace da su har suna kashe mutane 3 a cikinsu. Sauran kuma suka tsere da raunuka sakamakon harbin da suka sha.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng