Maryam Sanda: 'Yan sanda sun damke matar auren da ta halaka mijinta
- 'Yan sandan jihar Bayelsa sun kama wata mata, bisa zargin kashe mijinta da tayi
- Duk da dai wasu 'yan bindiga ne suka harbe shi a ranar Juma'a, wuraren layin Old Assembly Quarters
- Kamar yadda 'yan uwa da abokan arziki suka shaida, matar ta dade tana yunkurin kashe shi
'Yan sandan jihar Bayelsa, sun kama wata Eniye Zuokemefa Peter, bisa zargin kashe mijinta, Enebraye Zuokemefa Peter, wanda malami ne a kwalejin ilimin jihar Bayelsa, da ke Sagbama a kwanakin karshen mako.
An kama Mrs Peter ne a kan korafin da 'yan uwan mamacin suka gabatar wa hukuma a kan yunkurin kashe shi da tayi.
Dama ta zarge shi da rashin kamun kai saboda ta samu labarin ya haifi yara 2 da wata mata ba tare da aure ba.
Kakakin hukumar 'yan sandan, SP Asinim Butswat, ya ce sun kamata bisa ikirarin da ta taba yi a kan mijin nata, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Bidiyon dakarun sojin sama suna ragargaza 'yan bindiga a dajin Kuduru da ke Kaduna
Daily Trust ta tattara bayanai a kan yadda wasu 'yan bindiga suka harbe shi sau 3 a ranar Juma'ar da ta gabata bayan ya cire kudi a layin Old Assembly Quarters da ke wuraren Ekeki a Yenagoa, babban birnin jihar.
Wani dan uwan mamacin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce matar ta dade tana yunkurin kashe mijinta a kan zarginsa da haihuwa da wata mata, duk da bata taba haihuwa ba.
A cewarsa, "Auren nasu dama can yana ta girgidi, inda matar tana yawan yin yaji, amma ta koma bayan mijinta ya koma Yenagoa daga kasar waje."
Sannan an tabbatar da yadda wasu 'yan bindiga suka taba kai wa mamacin farmaki a cikin gidansa.
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)
"Ya dade yana fadawa 'yan uwa da abokansa cewa a damki matarsa idan wani abu ya sameshi," kamar yadda makwabtan suka ce.
Kungiyar matasa ta Ijaw ta bukaci jami'an tsaro da gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, su jajirce wurin gano wadanda suka kashe shi.
A wani labari na daban, wani mutum mai karancin shekaru, Roy Jairus Watuulo ya rasu washegarin daurin aurensu. Mutumin dan Kampala, kasar Uganda, ya zama angon kyakkyawar matar kenan, ashe rayuwa ba za tayi tsawo ba.
An daura aurensa da Anita Nabaduwa a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, washegari ajalinsa ya riske shi.
Bayan an gama shagalin aurensa, ya fara fadin yana jin alamun ciwo. Sai aka garzaya dashi asibiti da tsakar dare ya rasu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng