Tsohon dan takarar gwamna a jihar Kebbi ya rasu bayan gajeriyar jinya

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Kebbi ya rasu bayan gajeriyar jinya

- Manyan mutane da ma su fada a ji a jihar Kebbi sun halarci jana'izar Muhammad Sani Umar Kalgo

- Marigayi Kalgo ya rasu da safiyar ranar Talata bayan fama da gajeriyar rashin lafiya

- An yi sallar jana'izarsa a babban masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja

Tsohon mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi, Kalgo, da Bunza, Muhammad Sani Umar Kalgo, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya bayan gajeriyar jinya.

An yi Sallar jana'izarsa a Babban Masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Marigayi Kalgo ya taba neman takarar kujerar gwamnan jihar Kebbi gabanin zaben shekarar 2015.

Manyan mutane da suka hada da tsofin gwamnoni, ministoci, da manyan 'yan siyasa da masoya da magoya daga jihar Kebbi da fadin kasa.

KARANTA: Taron NEC: APC ta kori tsohon mataimakin Oshiomhole, ta rushe shugabancin shiyya da jihohi

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana'izarsa akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Sanata Adama Aliero, tsohon ministan tsaro, Dakta Bello Halliru.

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Kebbi ya rasu bayan gajeriyar jinya
Tsohon dan takarar gwamna a jihar Kebbi ya rasu bayan gajeriyar jinya
Asali: UGC

Tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), Honarabul Kabiru Tukura, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi) da sauransu.

KARANTA: Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC, Kwamred Abba Yaro

An haifi marigayi a ranar 15 Na watan Mayu, shekarar 1950, a karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi.

Marigayin ya rayu da mace daya da 'ya'ya biyar da suka hada da kwamishinan kasafi da tsarin tattalin arziki na jihar Kebbi, Dakta Abba Sani Kalgo.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce duk da kisan manoma 43 da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi a Zabarmari, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: