Jam'iyyar APC ta karbi bakuncin Sanata Ishaku Abbo a Hedkwatarta

Jam'iyyar APC ta karbi bakuncin Sanata Ishaku Abbo a Hedkwatarta

- Kwana daya da sauya sheka, Abbo ya kai ziyara sakatariyar sabuwar jam'iyyarsa

- Ya samu rakiyar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan

Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karbi bakuncin Sanatan da ya koma APC ranar Laraba a hedkwatar jam'iyyar dake Wuse 2, birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suke hedkwatar domin karban bakuncinsa sune shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Jam'iyyar ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita.

KU KARANTA: Ya tabbata Nigeria na cikin wani hali duba ga tsadar albasa, In ji Sarkin Musulmi

Jam'iyyar APC ta karbi bakuncin Sanata Ishaku Abbo a Hedkwatarta
Jam'iyyar APC ta karbi bakuncin Sanata Ishaku Abbo a Hedkwatarta Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

A jiya mun kawo muku cewa Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Ishaku Elisha Abbo, ya bayyana cewa ya sauya daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) domin yayi takara a zaben gwamnan 2023.

Sanatan ya bayyana cewa zai kayar da gwamna Ahmadu Fintiri a zaben jihar a 2023, Daily Trust.

Yayin hira da manema labarai ranar Laraba a majalisa, ya ce duk da cewa yayi yaki tukuru domin ganin Fintiri ya yi nasara a zaben 2019, gwamnan ya koreshi daga PDP bisa rashin iya mulkinsa kuma ya kawo rabuwan kai cikiin jam'iyyar.

"Gwamnan bai kayar da ni ba. Kora ta gwamnan yayi (daga PDP). Na fita ne kawai domin in kwace kujerar daga hannunsa," Sanata Abbo yace.

Elisha Ishaku Abbo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa masu rinjaye All Progressives Congress, APC.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana sauya shekan Abbo a wasikar da ya karanta ranar Laraba a zauren majalisa.

A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP be saboda salon mulkin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmed Fintiri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng