Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa

Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa

- Wani Roy Jairus Watuulo ya rasu washegarin daurin aurensa

- An daura aurensa ranar 5 ga watan Disamba, da safiyar Lahadi ya rasu

- Bayan an daura aurensa da sa'o'i kadan, ciwo ya kama shi ashe na ajali ne

Wani mutum mai karancin shekaru, Roy Jairus Watuulo ya rasu washegarin daurin aurensu. Mutumin dan Kampala, kasar Uganda, ya zama angon kyakkyawar matar kenan, ashe rayuwa ba za tayi tsawo ba.

An daura aurensa da Anita Nabaduwa a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, washegari ajalinsa ya riske shi.

Bayan an gama shagalin aurensa, ya fara fadin yana jin alamun ciwo. Sai aka garzaya dashi asibiti da tsakar dare ya rasu.

KU KARANTA: NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a

Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa
Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa. Hoto daga Lutoto Charity Martha
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu

Tuni 'yan uwa da abokan arziki suka fara wallafa hotunansa a kafar sada zumunta suna mai masa fatan rahama, da nuna tsananin tausayi ga matarsa.

Wani Wanyenya cewa yayi: "Ina yi wa matarsa addu'ar samun juriya a wannan lokaci mai tsanani."

Hanning Babyetsiza IV ta ce: "Yanzu haka hotunansa da na matarsa na shagalin aurensu suna wayoyinmu. Yanzu Roy ya mutu!"

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike, sun samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a sansaninsu da ke wuraren dajin Kuduru dake jihar Kaduna a ranar Asabar.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda, inda yace rundunar ta yi amfani da dabara ta musamman wurin kai hari ga 'yan ta'addan.

Fiye da 'yan bindiga 10 sojojin suka kashe a dajin, inda suka yi amfani da ISR wurin gano maboyar tasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: