Zanga-zangar EndSARS: Aisha Yesufu ta maida martani kan ƙarar da aka shigar dasu

Zanga-zangar EndSARS: Aisha Yesufu ta maida martani kan ƙarar da aka shigar dasu

- Zanga-zangar lumana ta ENDSARS da ta rikide zuwa rikici ta tafi ta bar 'baya da kura'

- Wani mutum mai suna Kenechukwu Okeke ya shigar da karar jagororin zanga-zangar

- Kafin faruwar hakan, babban bankin kasa (CBN) ya rufe asusun wasu mutane da kamfanoni bisa zarginsu da daukan nauyin zanga-zangar ENDSARS

Dr.Chinonso Egemba wanda aka fi sani da Aproko Doctor da ƴar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, sun maida martani kan ƙarar da Kenechukwu Okeke, ya shigar dasu akan marawa masu zanga-zangar EndSARS baya a faɗin Najeriya.

A ranar aTalata ne dai rahotanni suka fita cewa Okeke ya shigar da ƙarar akan masu goyawa zanga-zangar EndSARS baya a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Okeke lokacin da yake bayyana dalilin shigar da ƙarar yace yayi haka ne don wanzuwar tsaro,kare al'umma da kuma dawo da lumana a cikin al-umma.

Aproko lokacin da yake maida martani ya bayyana Okeke a matsayin Wawa.

KARANTA: Bayan Dangote, FG ta sake ware wani hamshakin dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakokin kasa

Ita kuwa Aisha Yesufu yayin da take maida martanin tace taji daɗin kasancewa cikin waɗanda aka shigar da sunanta cikin ƙarar.

Ta yabawa mai iƙirarin,Okeke da ya sanya sunanta a farkon waɗanda ya shigar da ƙarar.

Zanga-zangar EndSARS: Aisha Yesufu ta maida martani kan ƙarar da aka shigar dasu
Aisha Yesufu
Asali: UGC

Ta rubuta; "Farin cikina shine sun saka sunana dai-dai gurbin da ya dace, sunana ne na farko a jadawalin. Nagode muku masu zanga-zangar EndSARS.Ina alfaharin kasancewa a ɓangarenku."

Aproko a martanin da ya rubuta yace; "me yasa ake yiwa masu zanga-zangar EndSARS kallon kamar masu aikata laifi?

KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, sun yashe ma'adanar makamai

"Shin hakan na nufin laifi ne mutum ya yi magana akan zalunchin ƴansanda? Me yake Faruwa a ƙasar nan ne?"

"Shin mulkin dimokaraɗiyya muke ko kuwa kama karya? labari maras daɗin ji, labari mara ɗaɗin faɗa."

"Kenechukwu Okeke, kai wawa ne, kai barazana ne kuma abin kunya ga 'ƴancin ɗan adam' ba kamar yadda kake alfahari da hakan ba a sunanka.

"Kenechukwu, ba na jin komai sai tausayinka, tausayinka nake ji saboda idonka ya rufe, hankalinka ya gushe. Ka makance, ka ƙi ganin gaskiya.

"A ƙarshe dai kai wawa ne."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng