Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa

Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa

- Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara

- A ranar Juma'a ne kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin wata babbar kotu da ke Abuja a kan Sanda

- Alkali Halilu ya yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kamata da yayi da laifin kashe mijinta

Maryam Sanda, matar da kotu ta yankewa hukuncin kisa, za ta kara daukaka kara zuwa kotun koli don samun rangwamen hukuncin da aka yanke mata, ChannelsTv ta tabbatar.

Lauyanta wanda SAN ne, Joe Gadzama, ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Juma'a a Abuja.

Wannan ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yankewa Sanda, na kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe mijinta, Bilyaminu Bello da tayi.

KU KARANTA: Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram

Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa
Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa. Hoto daga ChannelsTV.com
Source: UGC

Marigayi Bilyaminu, wanda Maryam ta sharba wa wuka, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne, Halliru Bello.

Sanda ta ki amsa laifinta, inda tace kotu bata yi mata adalci ba, don bata aikata laifin da ake zarginta da shi ba.

A hukuncin da alkali Steven Adah ya dauki sa'o'i 2 yana yi, ya ce kotu ba za ta amince da kyale mai laifi ba, ba tare da ya fuskanci hukunci ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne, inda tace yayi daidai da sashi na 221 na laifuka, kuma hukuncin laifin shine kisa.

Kotun daukaka karar ta ce babu kokwanto, Sanda ce ta kashe mijinta kuma babu wani dalilin da zai sanya a ki amincewa da hukuncin kotun da ta baro.

Ya kara da cewa, tabbas Sanda ta kashe mijinta sakamakon ganin hotunan tsiraicin wata a wayarsa, sannan sai da ta tsorata shi tukunna.

Duk da wannan hukuncin, lauyan Sanda bai amince ba inda yace za su nufi kotun koli ko za su samu rangwame.

KU KARANTA: EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti

Idan za mu tuna, kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Alkali Yusuf Halliru ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020, jaridar The Cable ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel