Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda

- Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin da alkalin wata babbar kotu da ke Abuja ya yanke wa Maryam Sanda

- A watan Janairun wannan shekarar ne alkali Halilu ya yanke wa Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Ya yi hakan ne bayan kama ta da yayi da laifin kisan mijinta mai suna Bilyami Muhammed Bello

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Alkali Yusuf Halliru ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020, jaridar The Cable ta bayyana.

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda
Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda. Hoto daga Channelstv.com
Source: UGC

"Ta girbe abinda ta shuka, saboda an ce a kashe wanda ya kashe kuma duk wanda yayi kisa bai cancanci rayuwa ba," Halilu yace.

KU KARANTA: EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti

"Wacce aka kama da laifin ta cancanci kisa, a don haka na yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ta mutu."

Fusata da kuma rashin amincewa da Sanda tayi da wannan hukuncin ne yasa ta garzaya kotun daukaka kara domin bukatar sabon hukunci.

A bukatar da ta mika kotun daukaka karar ta hannun tawagar lauyoyinta, sun kwatanta hakan da tsabar rashin adalci.

KU KARANTA: Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

Ta bayyana cewa alkalin ya dogara ne da wasu irin shaidu wadanda basu hada da "tabbaci daga bakin wacce lamarin ya faru da ita, rashin makamin kisan, rashin shaida daga a kalla shaidu biyu da kuma rashin bayanin likita a kan musabbabin mutuwar."

Ta kara da bayyana cewa, alkalin ya yi kuskure inda ya dauka aikin dan sanda mai bincike kamar yadda ya bayyana a shafi na 76 na hukuncinsa.

Amma kuma, a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamban 2020, kotun daukaka karar ta jaddada hukuncin kisan a kan Maryam Sanda.

A wani labari na daban, kamar yadda rahotonni suka kammala, wadanda suka yi aika-aikan sun tsere da wayarsa, bayan sun sara saurayin wuri-wuri a jikinsa. Ya mutu ne ana hanyar kai shi asibiti.

Kawun mamacin, Thomas Ogisi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, inda yace mamacin ya yi caca ana saura mako daya a kashe shi, wanda yake sa ran zai samu naira miliyan 15 idan ya samu nasara.

Babu tabbacin an kashe shi ne saboda naira miliyan 15 din, tunda har yanzu ba a samu damar sanin halin da asusun bankinsa yake ciki ba, tunda 'yan ta'addan sun tsere da wayarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel