Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan APGA

Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan APGA

- Gwamna Willie Obiano, na jihar Anambra ya bayyana yadda tun da ya hau mulki ba a biya shi albashi ba

- A cewarsa, duk da yadda COVID-19 ta girgiza tattalin arzikin kasa, amma hakan sam bai dame shi ba

- Hasalima, ya dage wurin tsayawa tsayin-daka don tabbatar da walwalar ma'aikatan gwamnatinsa

Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya bayyana yadda tun da ya hau karagar mulki a 2014, ba a taba biyansa albashi ba.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ma'aikatan jihar Anambra jawabi a ofishinsu na Jerome Udoji da ke Awka, Daly Trust ta wallafa.

Kamar yadda Obiano ya tabbatar, ya cigaba da yin aiki tukuru don ganin sun samu cikakkiyar walwalar ma'aikatan jihar Anambra, kuma ya tabbatar kowa ya samu 'yan kudadensa ko wanne wata.

Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan PDP
Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan PDP. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a

A cewarsa, duk da matsanancin halin da kasar nan ta shiga, gwamnatinsa ta yi iyakar kokarinta wurin biyan albashi da sauran kudaden ma'akata, har da fansho da sauransu.

Gwamnan ya ce zai cigaba da ayyukan bunkasa jihar ta hanyar gyaran tituna da zarar harkokin arziki sun gyaru.

Obiano, wanda ya samu wakilcin HOS din shi, Barr. Harry Udu, ya ce Obiano ya yi iyakar kokarinsa wurin tabbatar da walwalar ma'aikatansa, musamman na jiharsa, inda yake kokarin biyansu albashinsu da wuri, sannan yana horar da ma'aikatan yadda ya dace.

KU KARANTA: Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce

Duk da yadda COVID-19 ta girgiza tattalin arzikin kasa, amma hakan bai sa yayi wa ma'aikatansa wasa da albashi ba. Gwamnatinsa ta cigaba da biyan albashi a ranar 25 na kowanne wata.

Sannan ana baiwa kowanne ma'aikacin jiha kyautar buhun shinkafa idan bikin kirsimeti ko na sallah ya yi.

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tanada duk wasu abubuwan da ya kamata ta samu don ta daukaka.

Ya fadi hakan a ranar Talata, lokacin da ya je wata kaddamarwa ta NASIDRC a Lafia, jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Inda yace Najeriya tana da duk wani abu da kasa take bukata, tana da masu fasaha, maza da mata, masu tunani da ma'adanai iri-iri wadanda ake nema don kasa ta daukaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: