Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara

Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara

- Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya ce bashi da matsala da Gani Adams

- A cewarsa, yanayin rayuwarsa da ta Adams ne ba su yi daidai ba

- Obasanjo ya ce sun hadu da Adams, amma ba wani batun shiryawa

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce a ciki da wajen gwamnati, ya hana Gani Adams, Aaare Ona Kakanfo na kasar yarbawa, kai masa ziyara, The Cable ta wallafa.

OPC, wacce Adams ya jagoranta ta janyo tashin hankali a jihar Legas a lokacin. Bayan nan ne 'yan sanda suka damki Adams, sannan suka rushe OPC.

Ya fadi hakan ne bayan ya ji ana yada cewa sun shirya da Adams bayan rikicin shekaru 15 da suka wuce, Obasanjo ya ce bashi da wata matsala da Adams.

Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara
Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi

An bayar da rahotonnin yadda suka hadu a gidan Ayo Adebanjo, wani shugaba na Afenifere, wata kabila da ke kudu maso yamma. Sauran shugabannin kungiyar sun samu halarta.

Amma a wata takarda da Kehinde Akinyemi, hadiminsa na harkar labarai ya bayar a maimakonsa, Obasanjo ya ce ziyarar da ya kai wa Adebanjo ba ta shiri bace.

"Tabbas gaskiya ne na kaiwa Cheif Ayo Adebanjo ziyara a gidansa da ke Lekki Phase 1 a ranar 2 ga watan Disamba kuma mun hadu da Gani Adams a can," kamar yadda Obasanjo yace.

"Ni ba na da wata matsala da Gani Adams, amma rayuwarsa ta baya ce ba ta yi daidai da tsarina ba. Tun a baya, lokacin ina kan mulki da kuma bayan saukata, na ki amincewa da ya kai min ziyara.

"Idan wani yayi tunanin ina da matsala da shi ko ita, kuma har ina bukatar shiri, tabbas a gidana da ke Abeokuta za a yi," yace.

KU KARANTA: Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon, Thisday ta wallafa.

A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da 'yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel