Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce

Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce

- Wata budurwa ta wallafa hotunan katafaren gidan da ta gina da albashinta wanda yake kasa da N50,000 duk wata

- Samke_nkwanyan ta wallafa hotunan a shafinta na Twitter, tana mai alfahari da ginin gidan da tayi da kanta

- A cewarta, ta gina katafaren gidan da albashinta na watannni 4 duk da N49,948.22 ne albashinta

Idan mutum yayi aiki tukuru, yana matukar alfahari wurin nuna wa duniya don a yi masa sam barka. Wata Samke_nkwanyan ta bayyana hoton wani katafaren gida da ta dage ta gina.

A cewarta, sai da tayi watanni 4 tana aiki tukuru tukunna ta samu nasarar karasa ginin gidanta. Da albashinta R2,000 wanda yayi daidai da N49,948.22.

A cewarta, dama ta tara R10,000 daidai da N250,000 a asusunta. Sannan ta amshi bashin R5,000 wato N124,975, wanda ta gama biya a watan Augusta. Duk da tarin da tayi, ta zage wurin yin aiki tukuru.

Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce
Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce. Hoto daga @Samke_nkwanyan
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yunwa da sanyi zai yi ajalinmu, Mata 'yan gudun hijira a Zamfara

Samke_nkwanyan ta ce ta bukaci taimakon 'yan uwa da abokan arziki amma suka ki taimaka mata.

Wata Layne_JazzeySA ta rubuta: "Gaskiya gidan yayi kyau, gaskiya kin yi kokari. Idan har da wannan albashin naki, kina iya gina gida, idan Ubangiji ya ciyar da ke gaba za ki iya yin manyan abubuwa. Cikin watanni 4, gaskiya kin yi kokari sosai."

tNaxe23 ya ce: "Ko karami ne ko babba, gidanki ne, kuma sunan ki zai amsa. Ki share duk wani wanda zai soke ki."

Haka dai mutane suka yi ta tsokaci iri-iri na yabo da gwarzontakar budurwar.

KU KARANTA: 'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tanada duk wasu abubuwan da ya kamata ta samu don ta daukaka.

Ya fadi hakan a ranar Talata, lokacin da ya je wata kaddamarwa ta NASIDRC a Lafia, jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Inda yace Najeriya tana da duk wani abu da kasa take bukata, tana da masu fasaha, maza da mata, masu tunani da ma'adanai iri-iri wadanda ake nema don kasa ta daukaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng