Hotunan dankareriyar doya da aka girbe a Anambra wacce ta mamaye mota daya
- Wani mutum mai suna Osita Amakeze, ya wallafa hotunan wata katuwar doya
- A cewarsa, an shuka doyar a wata gona da ke kauyen Agulu a jihar Anambra
- Mutane da dama sun yi ta mamakin irin wannan katuwar doya, mai ban sha'awa
Wani mutum mai suna Osita Amakeze, ya wallafa hotunan wata dankareriyar doya a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba wacce yace an nomata a kauyen Agulu, jihar Anambra.
A cewarsa, wannan doyar suke kira "ofu ji a ne-eme offload". Bayan ya wallafa hotunan doyar ne mutane da dama suka yi ta mamaki, kuma suna yaba wa girman doyar.
Dama a shekarar da ta gabata, ya wallafa hotunan wata doya wacce yace abokinsa ne ya noma ta. A cewarsa, doyar tana da nauyin 153.10 kuma duk kauyen su babu doya mai girmanta.
KU KARANTA: Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya
Mutane da dama sun yi ta tsokaci iri-iri a kan doyar, har wani Izuchuxy yana cewa: "Menene sirrin? Wacce iriyar doya ce wannan? Mutane nawa ne suka taimaka wurin nomata? A gaskiya wannan dankareriyar doya ce."
KU KARANTA: Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa
Wani Chabalus16 ya ce: "Wannan daya ne daga cikin abubuwan da nafi so idan nayi tafiya kauye don shagalin kirsimeti. Har na kosa inje in taya kakata hako doyarta."
Wani ccebuka kuwa cewa yayi: "Ban taba ganin katuwar doya irin wannan ba. Don Allah, menene sirrin?"
A wani labari na daban, a ranar Talata, kungiyoyin hadin kan arewa sun ce kashe-kashen da ake yi a arewacin Najeriya alama ce da ke nuna kuri'un da 'yan arewa suka kada wa shugaba Muhammadu Buhari a 2015 da 2019, sun zama asara.
A cewarsu, wannan harin da aka kai wa manoman jihar Borno, wadanda basu ji ba basu gani ba, alama ce wacce ta nuna cewa 'yan arewa sun yi kuskuren zabar Buhari.
A Wata takarda da kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman ya gabatar, ya ce yanzu Buhari ya zurawa 'yan arewa ido har rashin tsaro, talauci da mulkin kama-karya yayi ajalinsu gabadaya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng