Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye

Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye

- Sarki Lestsie III na Lesotho, shine mutum na 9 da yafi kowa mallakar filaye a duniya

- Duk da dai a tsarin kasarsu, ba a barin fili hakanan, ana baiwa mutane ne suyi noma

- Sarkin ya karanta shari'a a Ingila kafin ya koma kasarsu a nada shi a sarki yana da shekaru 56

Kamar yadda Africa Facts Zone ta ruwaito, Sarki Lestsie III shine mutum na 9 a kaf duniya, wanda yafi kowa mallakar filaye. Yana matukar alfaharin mallakar fili mai girman 11,720 square miles a Lesotho.

Abin lura shine, a kasarsa babu wani mutum da ya isa ya katantane fili ya bar shi hakanan, wajibi ne a bai wa mutane damar yin noma don a amfana.

Yana da shekaru 56, ya gaji sarauta a wurin mahaifinsa Mosheoshoe II, wanda yayi kaura a 1990.

Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye
Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye. Hoto daga thecommonwealth.org
Asali: UGC

KU KARANTA:Boye matar aure: Wata kotu a Kano ta bukaci Rarara da ya bayyana a gabanta

Duk da an maye gurbin mahaifinsa a 1995, Mosheoshoe III ya mutu a 1996 sakamakon hatsarin mota, sannan Lestie ya hau kujerarsa.

Ya yi karatunsa a Ingila a Ampleforth College.

Bayan nan, ya cigaba da karatu a National University ta Lesotho inda ya karanta shari'a.

KU KARANTA: Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda

A wani labari na daban, iyalan wani babban dan kasuwa daga jihar Katsina, Mahdi Shehu, sun bayyana irin hatsarin da rayuwarsa take ciki, a ranar Talata, inda suka ce tun bayan 'yan sanda sun kama shi, ba su sake ji daga shi ba.

Tun bayan Mahdi Shehu, wanda shine shugaban Dialogue Groups, ya zargi gwamnatin jihar Katsina da yin almubazzaranci da naira biliyan 52.6 daga asusun tsaron jihar a shekaru 5 da suka gabata, ya shiga cikin tashin hankali.

Wani daga cikin iyalansa, ya tattauna da Daily Trust a ranar Talata, inda yace ranar karshe da suka ji daga gareshi shine bayan maciji ya sare shi a harabar hedkwatar 'yan sanda dake Area 10 a Garki, Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel