Rundunar 'yan sanda ta magantu akan zargin coge da cuwa-cuwar hotunan ma su laifi

Rundunar 'yan sanda ta magantu akan zargin coge da cuwa-cuwar hotunan ma su laifi

- An zargi rundunar 'yan sanda da laifin amfani da fasahar zamani wajen harhada hotuna tare da wallafa su a zuwan na ma su laifi

- Jaridar TheCable ta rawaito cewa ta yi amfani da wata manhaja ta bin kwakwaf wajen tabbatar da cewa hotunan hadasu akai

- Sai dai, rundunar 'yan sanda ta ce ko kadan ba haka bane, ta na harhada hotunan ne domin saukaka wallafasu a matsayin labari

Rundunar ƴansanda ta fitar da jawabin martani a ranar Laraba dangane da hotunan masu laifi da ta wallafa a shafinta na Tuwita, wanda jama'a da dama su ka nunama shakku a kan sahihancinsu.

Rundunar ta ce an ɗauki hotunan a mabambantan wuri, amma an haɗe su wuri guda don sauƙaƙawa jama'a fahimta.

Jaridar TheCable ta wallafa rahoton cewa ta tabbatar da an yi amfani da fasahar zamani ta gyaran hotuna (Photoshop) a hotunan da hukumar ta saka a shafinta wajen sauya fasalinsu.

Hoton farko daga cikin hotunan na tsofaffinn fursunoni huɗu da suka tsere gidan yarin jihar Edo wato; Peter Osas, Onaruje Benjamin, Adebayo Opeyemi da Hudu Musa.

KARANTA: Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce

Hoto na biyu da suka wallafa shi bayan minti guda da sakin na farko wasu mutane biyu ne; Duleji Abubakar da Talatu Ibrahim waɗanda ake zargi da mallakar bindigu shida 6 ƙirar AK-47 a hannunsu.

Rundunar 'yan sanda ta magantu akan zargin coge da cuwa-cuwar hotunan ma su laifi
Rundunar 'yan sanda ta magantu akan zargin coge da cuwa-cuwar hotunan ma su laifi @Thecable
Asali: Twitter

Amma ga inda sarƙaƙiyar take:

Mutane huɗu dake jikin farko angansu sun yi tsayuwa kamar wasu fatalwu wanda hakan ke nuni da kuskure ƙarara, ba asalin hoton bane.

Sai dai, rundunar tace ko kusa ko alama hotunan bana ƙarya bane kuma ba abin da aka sauya bayan haɗe su wuri guda.

"An dauki hotunan a lokuta daban daban amma an haɗe su don samun sauƙaƙa kanun labaran ba tare da wahalar da hankulan jama'a ba." kamar yadda rundunar ta wallafa a Tuwita.

KARANTA: Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta

"Makaman da aka nuna a hoton, tabbas akwai su, kuma jami'anmu ne suka ƙwata daga hannun masu laifin."

Rundunar ƴansanda ta bayyana iƙirarin da jama'a ke yi a matsayin ƙage da shifcin gizo kan hotunan da ta wallafa a shafinta.

"Rundunar ƴansanda na sanar da ku cewa ba da gayya ko niyyar yaudara gami da wasa da hankalin jama'a ta yi hakan ba".

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa wasu miyagun 'yan ta'adda, da har ya zuwa yanzu ba'a tantance su waye ba, sun kashe babban jami'in dan sanda a yankin kudu maso kudu.

Dan sandan, Egbe Edum, mai mukamin mataimakin kwamishina, ya gamu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalinsa a jihar Kuros Riba.

'Yan ta'addar sun kai wa Edum hari da safiyar ranar Laraba a yankin garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng