Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce

Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce

- An hango wani bature farar fata cikin kayan ƴansanda bayan an watsa su a shafin sadarwar na Tuwita

- Wani mai amfani da shafin Tuwita wato @AfamDeluxo shine ya watsa hotunan a shafinsa,sai dai ba kowa ne ya yarda cewa jami'in ƴansanda bane

- A ɗaya daga cikin hotunan da aka watsa,an ga mutumin yayi tsaiwa irinta jami'an ƴansanda

Ganin wani bature farar fata ya jawo cece kuce a kafafen sadarwa na zamani bayan hotunansa cikin damara da kakin 'yan sandan Najeriya sun karaɗe yanar gizo.

A ɗaya daga cikin hotunan, an hangi mutumin ya tsaya da wani jami'in ƴan sanda.

Wasu masu amfani da shafin sadarwar Tuwita sun yarda cewa an ɗauki farar fatar aikin ɗan sanda, amma Legit.ng Hausa ba zasu iya tabbatar da sahihancin ko farar fatar jami'in ɗan sanda Najeriya ba ne.

Mutane sun maida raddin hotunan tare da tofa albarkacin bakinsu a kan hotunan. Wasu kuma sun yarda farar fatar jami'in ƴan sanda ne, sai dai wasu basu gamsu ba.

KARANTA: Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana

Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce
Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce @AfamDeluxo
Source: Twitter

Wasu na ganin cewa, a nasu ra'ayin, ko kadan bai dace a dauki farar fata aikin dan sanda a Najeriya ba.

A bangare guda kuma, wasu na ganin ba zai iya jure wahalar aiki da jama'ar Najeriya ba, musamman idan aka yi la'akari da kwatance da yadda aikin dan sanda ya ke da kima a turai da sauran kasashen da suka cigaba.

KARANTA: An tsayar da ranakun rubuta jarrabawoyin daukar aiki a NIS da NSCDC

Wani bangare na masu martani sun bayyana cewa akwai bakaken fata da ke aikin dan sanda a kasashen turai, a saboda haka mene ne abin mamaki idan farar fata ya zama dan sanda a Najeriya.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa wasu miyagun 'yan ta'adda, da har ya zuwa yanzu ba'a tantance su waye ba, sun kashe babban jami'in dan sanda a yankin kudu maso kudu.

Dan sandan, Egbe Edum, mai mukamin mataimakin kwamishina, ya gamu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalinsa a jihar Kuros Riba.

'Yan ta'addar sun kai wa Edum hari da safiyar ranar Laraba a yankin garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel