Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda

Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda

- Rundunar 'yan sanda ta kasa ta sanar da cafke wani gagarumin dan fashin motoci mai suna Gwamnati

- Ta sanar da yadda matashin mai suna Abdullahi Muhammed ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90

- Ya saba kwace wa jama'a motoci ta hanyar amfani da bindiga a jihohin Jos da Bauchi kafin a kama shi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wani mutum da ya kware wurin satar motoci ta hanyar saka wa mutane bindiga.

An gano barawon da ake kira da gwamnati ya yi fashin motoci 18 a cikin kwanaki 90 kacal.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, sunan matashin Abdullahi Muhammed amma an fi sanin shi da Gwamnati.

Ya kware a fashi da bindiga amma na motoci a cikin jihohin Jos da Bauchi kafin ya shiga hannun rundunar.

Rundunar 'yan sandan ta wallafa hotonsa a shafinta na Twitter bayan ta cafke shi.

KU KARANTA: Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak

Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda
Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda. Hoto daga @PoliceNG
Source: Twitter

KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Duk malamin da bai yi huduba a kan tsaro ba munafuki ne, Malam Maraya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin damar bayar da umarni ga 'yan sanda a kan kashe-kashe da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

A wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da gwamnan a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, El-Rufai ya bayyana damuwar da shi da takwarorinsa na sauran jihohi suka shiga a kan harkokin tsaron kasar nan.

Gwamnan ya ce ana kiran gwamnoni da shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai, amma a zahiri, basu da damar tankwara 'yan sanda.

Ya ce ba shi da damar neman 'yan sandan da za a tura jiharsa zuwa ga kwamishinan 'yan sandan jiharshi, da kuma bayar da umarni a kan harkokin 'yan sanda har sai Sifeta Janar ya yarda kuma ya bayar da umarni tukunna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel