Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin tarayya

Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin tarayya

- Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin tarayya

- Gwamnati ta ce iskar Gas ya fi sauki fiye da man fetur a farashi da kuma yafi kyau ga yanayi

Gwamnatin tarayya ta yi bayanin cewa yan Najeriya da suka mallaka mota zasu biya N250,000 domin a mayar musu da motocinsu masu amfani da iskar Gas maimakon man fetur.

A ranar Talata, Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya ce za'a mayarwa masu motoci milyan daya kyauta.

Amma yayin hira da shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV ranar Laraba, Justice Derefaka, mai bada shawara ga karamar ministan mai kan harkallar iskar Gas, Timipre sylva, ya yi bayanin cewa ba kyauta bane, mutane zasu biya kudi.

"Kudin da za'a biya ya danganta da irin motar da tukunyar Gas din za tayi amfani. Ga masu manyan motoci SUV, ya fi girma kuma za'a biya kimanin N200,000 zuwa N250,000 kuma yana fin hakan idan tukunyar motar shida ne, " yace.

Ya kara da cewa bai zama dole a biya dukkan kudin lokaci guda ba, mutum zai iya biya cikin watanni biyar zuwa bakwai.

"Kuma a haka, zai rage shan man ka da kimanin kashi 45 zuwa 50. Saboda haka ya fi sauki, " ya kara.

KU DUBA: An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi

Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin tarayya
Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin Credit: Carrogas Online/Getty Imagestarayya
Source: UGC

DUBA NAN: Budurwa ta kashe saurayinta bayan ya bukaci ta harbeshi don gwada maganin bindiga

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta bukaci mako daya kacal wajen kungiyar kwadago NLC domin duba yiwuwar janye karin farashin da akayiwa man fetur a watan Nuwamba.

Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana wannan bukatar ne a ganawarsu na ranan Alhamis a fadar shugaban kasa, rahoton The Nation.

Kyari ya bayyanawa NLC cewa kamfanin NNPC kadai ba zai iya janye farashin man ba ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel