Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure

Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure

- Wata mata mai suna Aminat, ta bukaci kotu ta raba aurenta mai shekaru 15, da yara 2 da mijinta Shehu

- A cewar Amina, idan Shehu ya bukaci kwanciya da ita tace ta gaji, yana watsa mata ruwa idan tayi bacci

- Ta ce har shaye-shaye yake yi a gaban yaransu, sannan yana dukanta da zarar ta yi masa dan kankanin laifi

Wata mata mai suna Aminat Isah, ta kai korafi ga Alkali Adeniyi Koledoye cewa mijinta yana barazana ga rayuwarta.

Matar ta bukaci kotu ta raba aurenta mai shekaru 15 da Shehu don ceton rayuwarta.

"Ku rabani da azzalumin mijina. Na dade ina cin bakar wahala a hannunsa. Duk lokacin da muka samu sabani dashi, ina rayuwa cikin tashin hankali.

"Tun farkon aurena dashi, karamin abu zan yi masa ya harzuka. Idan zai kwanta dani nace masa a gajiye nake, sai ya hau dukana.

Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure
Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

"Idan bai dakeni ba, sai ya jira na yi bacci tukunna, sai ya watsamin ruwa cike da bokiti. Na gaji da azaba," ta shaida wa kotu.

A cewarta, Shehu yana yin shaye-shayensa a gaban yaransu. Matar mai yara 2 ta ce mijinta bai damu da ita ba, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Kisan manoma 43 a Zabarmari: Zahra Buhari ta yi martani

"Mijina ko abinci baya bani, yana boye kayan abinci idan ya kawo su gidan. Har wata kwangila na samar masa a wurin wanda nake yi wa aiki, tunda dama aikin karafe yake yi, amma ya amshe kudin ya ki yin aikin.

"Bayan kamfanin sun fara matsamin lamba, haka nan na dage na biya kudaden. Akwai mutanen da ke zuwa har gidanmu don su yi rigima dashi saboda ya amshi kudin aiki a hannunsu kuma ya ki yi.

"Har biyan kudaden nake yi idan na ga ana shirin ci min mutunci," kamar yadda ta gabatar da korafin.

KU KARANTA: Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak

Ta kara da cewa mijinta baya girmama iyayenta. Ta bukaci kotu ta raba aurensu sannan ta bata damar rike yaranta.

Shehu ya ki zuwa kotun don ya amsa laifinsa ko kuma ya musa. Ya ki amsa duk kiran da kotu tayi masa.

Alkalin kotun, Koledoye, ya dage sauraron shari'ar zuwa 29 ga watan Disamba don yanke hukunci.

A wani labari na daban, ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da 'yan ta'adda saboda an hana ta makaman yakar 'yan ta'adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.

Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Alhaji Mohammed ya yi maganar ne a Makurdi yayin da ya kaiwa gwamna Samuel Ortom ziyara, inda yace 'yan ta'addan suna samun kudade daga kasashen ketare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: