Yunwa da sanyi zai yi ajalinmu, Mata 'yan gudun hijira a Zamfara

Yunwa da sanyi zai yi ajalinmu, Mata 'yan gudun hijira a Zamfara

- Mata masu gudun hijira daga kauyakun jihar Zamfara, sun ce sanyi da bakar yunwa za su iya ajalinsu, don suna cikin bala'i

- A cewarsu, 'yan ta'adda sun kone musu gonakinsu da gidaje, suna cikin wahala, yaransu kullum cikin kuka suke

- Fiye da mata 500 suka tsere daga kauyakun jihar Zamfara zuwa sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Kebbi, saboda 'yan bindiga

Mata masu gudun hijira daga kauyakun jihar Zamfara sun ce yunwa da sanyi zai iya ajalin su da yaransu, bayan 'yan bindiga sun kone musu gidajensu.

BBC Hausa ta ruwaito yadda fiye da mutane 500 daga kauyukun karamar hukumar Maru suke ta gararamba a tituna da sansanin gudun hijira na garin Mai Rairai, da ke jihar Kebbi.

Matan da suke sansanin 'yan gudun hijira tare da yaransu, sun ce ba su da abinci kuma 'yan bindiga sun kone musu gonakinsu, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure

Yunwa da sanyi zai yi ajalinmu, Mata 'yan gudun hijira a Zamfara
Yunwa da sanyi zai yi ajalinmu, Mata 'yan gudun hijira a Zamfara. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Kanin tsohon dan majalisa ya jigata bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a hanyar Kaduna zuwa Zaria

Jiya BBC Hausa ta tattauna da daya daga cikin matan, wacce ta je sansanin tun daga Dankofa tare da yaranta 15, inda tace suna rayuwa cikin matsananciyar yunwa a sansanin 'yan gudun hijira, kuma yaransu kullum cikin kuka suke.

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon.

A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da 'yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.

A cewarsa: "Akwai mutanen da za su tuna lokacin da Janar Gowon ya bar Najeriya da rabin kudin CBN, kuma ya tare a Landan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel