Kanin tsohon dan majalisa ya jigata bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a hanyar Kaduna zuwa Zaria

Kanin tsohon dan majalisa ya jigata bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a hanyar Kaduna zuwa Zaria

- 'Yan bindiga sun kara kai wani hari a hanyar Kaduna zuwa Zaria a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba

- Cikin matafiyan da suka tsare har da dan uwan wani tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Igabi

- Har sun ji masa miyagun raunuka, yanzu haka yana asibitin sojoji na 44 ana kulawa da lafiyarsa

'Yan bindiga sun kai wa dan uwan wani tsohon dan majalisa farmaki a hanyarsa ta Kaduna zuwa Zaria, inda suka bude masa wuta.

A ranar Lahadi, 30 ga watan Nuwamba, 'yan bindiga suka tsare ababen hawa a wuraren Kwanar Tsintsiya da ke karamar hukumar Igabi ta hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Cikin matafiyan har da dan uwan Alhaji Kabir Muhammad, dan uwan Hon. Muhammad Abubakar Mamadi, tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Igabi.

Kanin tsohon dan majalisa ya jigata bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a hanyar Kaduna zuwa Zaria
Kanin tsohon dan majalisa ya jigata bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a hanyar Kaduna zuwa Zaria. Hoto daga Umar Rigasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Al-Mustapha Abacha ya fallasa shirin wasu shugabanni na tarwatsa Najeriya

Yanzu haka yana asibitin 44 na sojoji da ke Kaduna ana kulawa da lafiyarsa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarada ranar Litinin.

Ya ce bataliyar rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar ritsa 'yan ta'addan, inda suka kashe 1, sauran kuma suka tsere da raunuka sakamakon ragargazar da suka sha da alburusai.

KU KARANTA: Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed

A wani labari na daban, sakamakon kashe-kashen da 'yan Boko Haram suke tayi a Najeriya, 'yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan wata wallafarsa da yayi a 2015 a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Lokacin da Osinbajo yake kamfen a 2015, ya wallafa; "Idan shugaban kasa yace ba zai iya kulawa da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma ba, tabbas laifi ne da yayi wanda ya cancanci a tsigeshi."

Ya yi wannan wallafar ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2015, wanda mutane suka yi ta tsokaci suna yabonsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel