An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai

An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai

- Hukumar Soji ta hukunta wani babban jami'inta kan saba dokar amfani da kafafen sada zumunta na zamani

- An hukunta Janar Adeniyi tare da hadimin na musamman

- Sojan ya lashi takobin daukaka karan hukuncin da aka yanke masa

Wata kotun Sojoji dake zamanta a Abuja ta kama Manjo Janar, Olusegun Adeniyi, tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, da laifi.

Kotun ta rage masa matsayi da shekaru uku.

Adeniyi, wanda Manjo Janar ne ya bayyana a wani bidiyo a watan Maris inda yake kuka kan rashin makaman yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Daya daga cikin wadanda suke tare da shi suka saki bidiyon a yanar gizo.

Ba tare da bata lokaci ba aka cireshi daga matsayin kwamandan Operation Lafiya Dole kuma aka tura shi cibiyar dukiyoyin sojin Najeriya dake Abuja.

Daga baya aka mayar da shi hedkwatar Soji dake Abuja inda yake gurfana a kotun Sojoji.

Yayin yanke hukunci kansa ranar Litinin, kotun ta kama Adeniyi da laifin saba ka'idojin gidan Soja kuma ta bada umurnin rage masa matsayi da shekaru akalla uku, The Cable ta ruwaito.

Hadiminsa, Tokunbo Obanla, wanda aka gurfanar da su tare da Janar, shi ma an kama shi da laifi kuma an yanke masa hukuncin daurin makonni hudu a kurkuku da mugun wahala.

Lauyoyin Adeniyi sun ce zasu daukaka kara gaban wata kotun.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta tabbatar Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC

An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai
An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai Hoto: @thecable
Asali: Twitter

DUBA NAN: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami Buratai, Sadiqu Baba, dss

A wani labarin kuwa, gwamnatin tarayya za ta taka wa duk wani mai zanga-zanga a kan cutarwar dan sanda da wasu matsololi makamantan haka burki, jaridar Thisday ta ruwaito.

Ta ce duk wanda ya gwada kawo cikas ga zaman lafiya ko kuma harkar tsaron kasa zai kwashi kashinsa a hannu.

Gwamnatin tarayya ta zargi za a fara wani sabon zanga-zanga na EndSARS a ranar 5 ga watan Disamba, wanda yake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel