Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF

Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF

- Shugaban PGF, Dr. Salihu Lukman, ya alakanta rikicin cikin jam'iyyar APC da hadamar 'yan jam'iyyar wurin neman mulki

- A cewarsa, in dai har jam'iyya bata tsaya tsayin-daka wurin dakatar da 'yan adawar cikinta ba, za ta iya durkushewa

- Ya fadi hakan ne a wata takarda wacce ya gabatar ranar Lahadi a Abuja wacce ya bayyana musabbabin rikicin cikin APC

Darekta janar na PGF, Dr. Salihu Lukman, ya alakanta rikicin cikin jam'iyyar APC da dagewar wasu jiga-jigan jam'iyyar wurin gasa da juna, jaridar The Punch ta wallafa.

Ya bayyana hakan a wata takarda mai taken, "Demokradiyyar Najeriya da gasar tsayawa takara cikin jam'iyya," a Abuja ranar Lahadi.

PGF wata kungiya ce ta gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC. Salihu Lukman shine shugaban kungiyar baki daya.

KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Bashir Ahmad yayi ga matarsa ranar zagayowar haihuwarta

Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF
Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A cewarsa, "Cikin matsalolin da Najeriya take fuskanta yau har da matsalar gasa cikin jam'iyya wurin neman kujera. Mafi yawan shugabannin jam'iyya suna dagewa wurin gasa."

A cewarsa, rawar da jam'iyyu suke takawa wurin durkusar da abubuwan da ba zabinsu bane, shine dalilin da yasa ake samun adawa har a cikin jam'iyyu.

Duk wanda yake son tsayawa takara, wajibi ne ya nemi hadin kan 'yan adawar cikin jam'iyya don su taru su mara masa baya, kafin ya tunkari jam'iyyoyin adawa.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci a basu damar gurfanar da 'yan ta'adda

A cewarsa, yadda jam'iyyoyi suke kawo cibaya a harkokin mulki babbar matsala ne. Yace daga ciki har wajen jam'iyya suna janyo durkushewar mutane da kuma cigaban siyasa.

Lukman ya bayyana yadda mafi yawan shugabanni da cigaban siyasa har da na jam'iyyu suke gaza samun nasara idan basu dakatar da matsalolin cikin jam'iyya da kuma canjin shugabanci."

A wani labari na daban, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa a kan yadda APC suka zarge shi da shirye-shiryen neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP don zaben 2023.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bai tattauna da wani a kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel