Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado

- Akwai sarakuna masu ado da salo na musamman a Najeriya

- Duk da sarakuna ne, sun dade suna tafiya da hankulan 'yan mata

- Suna sanya sutturu na gargajiya a zamanance masu birgewa

Duk munin suttura, akwai yadda mutum zai sanya su fito su birge duk mai kallonsa. Akwai sarakuna masu salo da dama a fadin kasar nan. Yanayin saka suturunsu abun dubawa ne.

1. Oba Adeyeye Ogunwusi

Kyakkyawan sarki, mai izza da kwarjini sannan mai kyawun lafazi, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, yana daya daga cikin sarakuna masa salo da takun ban girma.

Idan aka yi batun saka suttura kuwa, musamman sutturun gargajiya na sarauta, ba a bar shi a baya ba. Yawancin suturunsa farare ne domin suna dacewa da kyawunsa.

Yana sanya sarkoki na tsadaddun duwatsu a wuyansa da hannayensa, masu kaloli mabambanta da samfari.

Batun takalma kuwa, yana sanya na fatoci ne masu kayatarwa.

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado
Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado. Hoto daga en.wikipedia.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan manoma 44 a Borno: Gwamnatinmu ta yi iyakar kokarinta, Buhari

2. Oba Saheed Elegushi

Elegushi na Ikateland, Oba Saheed Elegushi mutum ne mai tabbatar da bashi da makusa idan zai fita. An nada shi mulki tun yana da shekaru 34 a duniya, yana daya daga cikin sarakuna masu karancin shekaru.

Mutum ne shi mai sanya sutturu masa kayatarwa, yana sanya fararen kaya da wasu kaloli kamar koraye, ruwan bula, jajaye da kalar ruwan kasa.

Yana sanya jallabiyu musamman farare, idan kuma zai fita taro na daban, yana tsukewa da sutturu irin na zamani. Ya fi sanya bakaken takalma musamman na fata.

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado
Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado. Hoto daga Thisday.com
Asali: UGC

3. Ambasada Ahmad Bamalli

Sarkin Zazzau Bamalli, yana daya daga cikin sarakuna masu sanya sutturu na ban mamaki da burgewa.

Duk da bai dade da hawa karagar mulki ba, amma kowa ya san shi da aji da kayatarwa. Yana sanya alkyabbu masu birgewa da tabarau da zobba masu kyau.

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado
Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

4. Obi na Issele Uku

Obi Nduka Ezeagwuna yana daya daga cikin sarakuna masu kamun kai. Yana sanya sutturu marasa hayaniya amma masu aji.

Da zarar ya shiga wuri, kyawun fuskarsa ne yake fara haskawa, shiyasa kowa yake lura dashi. Ya fi sanya fararen sutturu sai sarka mai tsadaddun duwatsu. Kuma duk sutturun da ya sanya sai sun yi masa kyau.

KU KARANTA: 2023: Jigon APC ya bayyana matsayar Buhari a kan takarar Goodluck Jonathan

5. Sarkin Kano Aminu Bayero

Sarki Aminu na Kano ba a bar shi a baya ba idan aka zo maganar sanya sutturu masu kayatarwa. Duk sutturun da za ka ga Bayero da su yawanci tsadaddu ne. Idan ya sanya su, suna zama a jikinsa tamkar saboda shi aka kirkiresu.

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado
Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado. Hoto daga @masarautarKano
Asali: Twitter

6. Oba Abdulrasheed Akanbi

Shine Oluwo na Iwuland, mutum ne mai salo na musamman, dakyar mutum ya dube shi bai kara kallo ba don yana sanya kaya masu birgewa.

Yana zabar kaloli da salo na daban. Sannan yana sanya huluna masu duwatsu wadanda suke daukar ido.

Bakin gilashinsa kuwa yana kara masa kyau mai daukar hankali. Sannan idan aka zo batun takalma ba a bar shi a baya ba, yana sanya takalma masu daukar ido.

Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado
Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado. Hoto daga Naijaloaded.com
Asali: UGC

A wani labari na daban. budurwar mai karancin shekaru, ta yi wannan wallafar a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda take bayyana abubuwan alfahari dangane da ita.

Budurwar mai sayar da kaji a kasuwar wuraren Abakpa Nike da ke jihar Enugu, ta tallata hajar ta a Facebook, inda tace za su siyan kajin wurinta don shagulgulan karshen shekara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel