2023: Atiku ya sanar da matsayarsa a kan takara kujerar shugabancin kasa

2023: Atiku ya sanar da matsayarsa a kan takara kujerar shugabancin kasa

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo

- A cewarsa, kullum yawan 'yan jam'iyyar karuwa yake yi, amma taron tsitsiya ne babu shara

- Ya ce maimakon 'yan APC su mayar da hankulansu wurin gyara kasa, sun tsaya gutsiri-tsoma

Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa a kan yadda APC suka zarge shi da shirye-shiryen neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP don zaben 2023.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bai tattauna da wani a kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Atiku ya yi wannan maganar ne ta hadiminsa na bangaren yada labarai, Paul Ibe, inda yace ya kamata jam'iyya mai mulki ta mayar da hankali a kan matsalolin da kasa take fuskanta, ba wai gutsiri-tsoma ba.

2023: Atiku ya sanar da matsayarsa a kan takara kujerar shugabancin kasa
2023: Atiku ya sanar da matsayarsa a kan takara kujerar shugabancin kasa. Hoto daga Atiku Abubakar
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Bashir Ahmad yayi ga matarsa ranar zagayowar haihuwarta

Ya ce a wannan mawuyacin hali da Najeriya take ciki, a karkashin mulkin APC, kamata yayi a ce ta tattara hankalinta tsaf ta mayar wurin taimakon Najeriya da 'yan Najeriya, ba wai cece-kuce da yin tsegumi a kan PDP ba.

Kamar yadda Atiku yace: "Alamu duk sun bayyana cewa APC ta kasa tabuka komai cikin abubuwan da tayi kamfen a kan PDP a 2015.

"Tun daga talauci zuwa harkar tsaro; rashin ayyukan yi zuwa tsadar rayuwa; hadin kan 'yan kasa zuwa mummunan suna a kasashen ketare; tozarta hakkin bil'adama zuwa talauci da fatara- matsalolin da in dai har jam'iyyar APC tana son talakawa a yadda ta nuna, ya kamata tayi wani abu akai."

KU KARANTA: Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya

Atiku ya zargi jam'iyyar APC da kara yawan 'yan jam'iyya amma babu mayar da hankali zuwa gyara matsalolin kasa. Ya bayyana matsalolin da gwamnatin APC ta janyo wa Najeriya.

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta jihar Legas ta fara fuskantar rabuwar kawuna cikin manyan 'yan jam'iyyar. Olajide Adeniran, ya zargi gwamnatin jihar ta yanzu da damawa da mutane kalilan.

A wani taro da suka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, inda ya sanar da burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar da zarar Babajide Sanwo-Olu ya sauka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng