Gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci a basu damar gurfanar da 'yan ta'adda
- Shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabas, Farfesa Babagana Zulum, ya koka a kan halin da yankinsu yake ciki
- Ya bukaci gwamnatin tarayya ta basu damar hukunta duk wani dan ta'adda ko mai garkuwa da mutane da suka kama a yankinsu
- A cewarsa, daukan dan ta'adda ko mai garkuwa da mutane tun daga yankinsu zuwa Abuja yana matukar bada wahala
Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci gwamnatin tarayya ta bai wa jihohinsu damar yankewa duk wanda aka kama da laifin ta'addanci hukuncin da ya dace dashi.
Gwamnan jihar Borno, kuma shugaban kungiyar, Babagana Umara Zulum ne ya bukaci hakan a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Yola, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Zulum ya koka a kan yadda Antoni janar na tarayya ne kadai yake da damar yankewa 'yan ta'adda hukunci. Ya ce daukar 'yan ta'adda daga yankinsu har zuwa Abuja don yanke hukunci yana matukar bayar da wahala.
KU KARANTA: Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban
KU KARANTA: 'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina
Ya bayyana irin damuwarsa a kan yadda ta'addanci da garkuwa da mutane yake hauhawa a yankinsa, inda Zulum ya bukaci a basu damar yankewa duk wanda aka kama da laifi hukunci don tsare rayukan al'umma.
"Wadannan matsalolin suna kara ninkuwa a yankin arewa maso gabas, sannan kullum suna kara haurawa jihohi masu makwabtaka da su. Ta kai ga mutane su na tsoron bin manyan tituna saboda tsoron 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane," a cewarsa.
"Ya kamata a kalli halin da muke ciki, a bamu damar yanke wa duk wani dan ta'adda hukunci dakanmu, don mutanenmu su samu cikakkiyar kariya idan za su bi hanyoyi."
Ya kuma bukaci kungiyar ta duba masu wa'azin da ke wuce gona da iri, masu zuga 'yan ta'adda don su cigaba da ta'addanci.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya lura da yadda kungiyar ta jajirce wurin kawo zaman lafiya a arewa maso gabas, sannan ya bukaci ta kara kokarin samar da hanyar taimakon duk wasu masu gudun hijira.
A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta tabbatar da yadda kwanan nan za ta kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar soji. A cewarsa, ta yadda sojoji suke ragargazar 'yan ta'adda, kwanan nan za su zama tarihi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng