Kalamai masu ratsa zuciya da Bashir Ahmad yayi ga matarsa ranar zagayowar haihuwarta
- Bayan watanni kadan da aure hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ranar haihuwar amaryarsa ta zagayo
- Ahmad ya wallafa hotonsa tare da matarsa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter
- Baya ga hoton, ya wallafa wani tsokaci, wanda yake nuna matukar kaunar da yake yi wa amaryarsa
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya wallafa hotunan matarsa, Naeemah Junaid a shafinsa na Twitter, inda yake tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Kamar yadda ya wallafa:
"Barka da zagayowar ranar haiwuwar ta musamman di na, babbar kawata, matata, @naeemah_,
"Ina farincikin faruwar abubuwan da suka janyo na hadu da ke a rayuwata. Ina matukar kaunarki kuma zan cigaba da sonki. Ina miki fatan kara ganin shekaru cike da farinciki da kauna, Masoyiyata."
KU KARANTA: Cikin kwanakin nan za mu kawo karshen ta'addanci, Hedkwatar tsaro
A watanni kadan da suka gabata ne aka sha shagalin bikin Bashir Ahmad da kyakyawar amaryasa, Na'eemah Junaid Bindawa.
Hadimin shugaban kasan ya garzaya tare da tawagarsa har zuwa jihar Katsina inda aka daura aurensa da rabin ran sa.
Babu shakka jhar Katsina ta cika damkan da manyan mutane masu cike da izza.
Bayan nan, tawagar ta kwasa inda suka zarce jihar Kano domin yin wata kasaitacciyar liyafa wacce ta matukar birge masoyansu.
KU KARANTA: Da duminsa: Bidiyon 'yan fashi da makami suna balle banki, sun kwashe makuden kudade
A wani labari na daban, jami'an tsaro na farin kaya na jihar Katsina sun damki wani miji da matarsa da miyagun makamai.
Ana zargin Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar da ta'addanci. Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da sojoji suka yi.
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin a kauyen Abukur da carbi 14, caliber ammunition rounds 61 na 9.6mm da special ammunition rounds 399 na 7.62mm.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng