Hudubar Murtadha Gusau: Babu rikici ko ta'addanci a addinin Musulunci
- Kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci, jaridar Premium Times ta wallafa hudubar Malamin addinin Musulunci, Murtadha Gusau
- A cikin hudumar, Malamin ya yi kira tare da yin nuni a kan yadda addinin Musulunci ya bawa zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama'a muhimmanci
- Murtadha ya kawo hujjoji daga cikin Qur'ani da Hadithai daban-daban a cikin hudubar tasa
Da sunan Allah mai rahama,mai jinƙai. Dukkan kirari da yabo sun tabbata ga Allah, Allah ka ƙara albarka ga manzo fiyayyen halitta, iyalansa, sahabbansa da dukkan waɗanda suka hau tafarkinsa har zuwa ranar sakamako.
Ya ku ƴan'uwa maza da mata, ku sani, addinin Musulunci yana kula da yaɗa zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin al-umma bakiɗaya.
Haka zalika Addinin musulunci yai hani ga dukkan hargitsi,faɗa,tarzoma,tashin hankali da dukkan nau'in faɗa da ta'addanci,wannan ya saɓawa koyarwa da kimar addinin musulunci.
Allah maɗaukakin sarki yana cewa; "Aikin kirki da sharri ba ɗaya suke ba.Ku aikita mafi kyawu, sai kuga maƙiyanku sun dawo abokanka mafi soyuwa agareku."(Ƙur'ani 41:34).
KARANTA: An dawowa da Nigeria gunkin Ife Terracotta mai shekaru 600 daga kasar Netherlands
Halayyan manzo da yake aikitawa sun isa misalin wannan ayar.
Al-umma da annabi Muhammad (SAW) ya zauna cikinta ba ta sha ban - ban da irin tamu al'ummar ba. Akwai tashe tashen hankula da ta'addanci har a wancan lokacin.
Ana yin su kamar an yarje ayi hakan, kuma zamu iya ganin hakan daga maganar Jabir ɗan Abu Talib wanda ya yi nada Najjashi sarkin Habasha.
"Ya kai sarki, mu mutane jahilai na jahiliyya da rashin ɗa'a, masu bautar gumaka da cin naman matattun dabbobi, masu aikita kowanne irin laifi da abin kunya, muna raba dangantakar jini, muna tozarta baƙi, sannan masu ƙarfinmu suna zaluntar marasa ƙarfi." (Sira ibn Hisham).
KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Idan muka ɗau matsalar kashe ƴa'ƴa mata kawai zamu yadda hakan yayi kamanceceniya da tashin hankali da ta'addanci,wannan shine dalilin da yasa Annabi(SAW) yayi magana akai.
A tsakiyar wannan hali ne, Annabi Muhammad (SAW) ya zo ya samarwa al-umma mafita daga ta'addanci da tashin hankali.
Tsarin Musulunci ya zo da hikima, dabaru da jinƙai. Matakin farko na mafitar shine;
"Ku bautawa Allah kamar kuna ganinsa, idan ku bakwa ganinsa, to shi yana ganinku".(Ahmad)
Daga nan sai Annabi ya ɗauki mataki na biyu ta hanyar maida al'umma tafarkin rayuwa irinta ɗan adam wacce ya cancanta ya rayu bisa tafarkinta".
Akwai ɗabi'un da dole sai al'umma sun bi su, na farko dai shine; yaɗa halayen kirki, mutunci, da yin adalci ba tare da nuna bambancin addini, ƙabila, yanki, ko launin fata ba.
Annabi (SAW) yana cewa; "Allah mai jinƙan bayi ne, kuma yana son masu jinƙai, Allah baya son tashin hankali ko wani abu makamancinsa" (Muslim).
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Najeriya ta riƙe kambunta na kasancewa ƙasa ta uku wadda ta'addanci ya yiwa katutu a duniya, a cewar ƙungiyar ƙididdigar ta'addanci ta duniya (GTI).
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng