CACOVID ta sanar da sabon shirin da zata bullo dashi na tallafawa matasa da 'yan kasuwa

CACOVID ta sanar da sabon shirin da zata bullo dashi na tallafawa matasa da 'yan kasuwa

- Gamayyar kungiyoyi masu yaki da annobar korona, CACOVID ta ce zata tallafawa matasa da 'yan kasuwa a Najeriya

- Hakan na zuwa ne bayan banar da 'yan daba suka yi a wasu jihohin Najeriya yayin zanga zangar EndSARSs

- Ayyukan da CACOVID zata yi sun hada da samar da cibiyoyin lafiya, bada kayayyakin abinci, da sauransu don tallafawa gwamnati

Gamayyar kungiyoyi masu masu yaƙi da COVID-19 (CACOVID) a Najeriya, sun sanar da bayanan cigaban ayyukansu da kuma niyyarsu ta tallafawa gwamnati a ƙoƙarin sake gini don farfaɗo da tattalin arziƙin kasar.

Hakan ya biyo bayan tashin hankalin da ƴan daba waɗanda suka gwace ragamar zanga-zangar EndSARS suka haddasa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

CACOVID ta sanar da sabon shirin da zata bullo dashi na tallafawa matasa da 'yan kasuwa
CACOVID ta sanar da sabon shirin da zata bullo dashi na tallafawa matasa da 'yan kasuwa. Hoto daga @Vanguardngr
Asali: UGC

Zanga-zangar wadda ta jawo asarar rayuka ,dukiyoyi da tsayawar al'amura cak a jihohin da abin ya shafa.

DUBA WANNAN: 'Yansanda sun yi ram da wata mata mai bawa ƴanfashi, ɓarayi da masu laifi mafaka

Lokaci da ake fayyace kuɗaɗen da CACOVID ta kashe, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin ƙasa, ya bayyana cewa ƙungiyar ta bada gudunmawar kuɗaɗe maƙudai.

"Ƙungiyar ta karɓi naira biliyan 39.64 a matsayin gudunmawa daga mambobinta, sannan ta kashe naira biliyan 43.272 a tsare tsare da ayyuka daban daban.

Ayyukan sun haɗar da, gina cibiyoyin lafiyar ware masu cuta na naira biliyan 4.194, da kashe naira biliyan 9.017 wajen siyo kayan aikin lafiya da magunguna.

Sai naira biliyan 28.7 da aka kashe a kayayyakin abincin tallafi, gami da wayar da kan al-umma a jihohin Najeriya ta hanyar kafafen yaɗa labarai.

KU KARANTA: An dawowa da Nigeria gunkin Ife Terracotta mai shekaru 600 daga kasar Netherlands

Emefiele ya bayyana cewa CACOVID ta ɗauki matakan ne a matsayin tallafawa gwamnati don sauƙaƙawa gwamnati farfaɗo da tattalin arziƙinta wanda annobar ta girgirza da kuma fargarbar da aka shiga kwanan nan.

Da yake magana akai Gwamnan Babban Bankin, ya ce;

"Wannan yunƙuri na daga cikin muhimman matakai ne na gina gaskiya tare da daƙile tashin hankali anan gaba cikin al'ummarmu.

"Zai kuma dace da ƙoƙarin da gwamnati keyi don samarwa matasa aikinyi da kuma ƙa."

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng